Koma ka ga abin da ke ciki

Daga hagu zuwa dama: Dan’uwa Ivan Puyda a cikin wani keji a kotu, sai mahaifinsa Dan’uwa Grigoriy Puyda, da kuma kakansa Dan’uwa Pyotr Partsey

14 GA OKTOBA, 2020
RASHA

Yaro da Mahaifinsa da Kuma Kakansa Sun Rike Amincinsu Duk da Tsanantawa

Yaro da Mahaifinsa da Kuma Kakansa Sun Rike Amincinsu Duk da Tsanantawa

Dan’uwa Ivan Puyda yana jiran hukuncin da za a yanke masa ba tare da jin tsoro ba. Misalin mahaifinsa da kakansa ne suke taimaka masa ya rike amincinsa

Dan’uwa Ivan Puyda yakan tuna lokacin da babansa yakan dawo gida da yamma kuma ya karanta masa da ’yan’uwansa bakwai Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. Ya tuna lokacin da shi da mahaifinsa Grigoriy, sukan yi wa’azi a kauyensu, Kvitok, har su je gidajen malamansa da ’yan ajinsu. A lokacin da Dan’uwa Puyda yake matashi, shi da kakansa Pyotr Partsey sukan je wa’azi a yankin da ba a sanya ma kowa ba. Hakan ya taimaka masa ya ga irin kwazo da halin sadaukarwa da kakansa yake da shi.

Dan’uwa Puyda ya ga yadda mahaifinsa da kakansa suke karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da kungiyarmu ta wallafa. Don haka, ya kudura cewa zai bi sawunsu.

Yanzu shekarun Dan’uwa Puyda 41 kuma yana bin sawunsu, amma a hanyar da bai yi tsammani ba. An kama shi an kai shi kurkuku domin yana bauta wa Jehobah. A ranar 30 ga Mayu, 2018 ne jami’an tsaron Federal Security Service (FSB) suka kama shi kuma suka tsare shi a kurkuku na tsawon watanni hudu. Bayan an sake shi, sai aka tsare shi a gidansa har tsawon watanni shida. An kai kakansa Dan’uwa Partsey kurkuku a lokacin mulkin gwamnatin Nazi da kuma lokacin mulkin gwamnatin Tarayyar Soviet. Mahaifinsa Grigoriy Puyda ma, an kai shi kurkuku a lokacin mulkin Tarayyar Soviet.

Dan’uwa Ivan Puyda ya ce: “A 2 Timoti 3:​14, manzo Bulus ya ce: ‘Ka ci gaba da abin da ka koya, ka kuma tabbatar da gaskiyar koyarwar, gama kana sane da wadanda ka same koyarwar daga gare su.’ Tuna da wadanda suka koya min gaskiya yana karfafa ni. Babu gwamnati ko kurkuku da ya iya sa su su musanta imaninsu, kuma tsanantawa za ta zo ta wuce. Yanzu, ina bin abin da suka koya min kuma zan ci gaba da bin sawunsu. Na san idan na rike amincina, Jehobah zai ci gaba da taimaka min.” Dan’uwa Ivan Puyda yana jira ya ji irin hukuncin da za a yanke masa.

Ya ce a duk lokacin da mahaifinsa da kakansa suke gaya masa labarin yadda rayuwa take a kurkuku, ba sa ambata irin wahalar da suka sha a wurin. Abin da suke fada shi ne yadda suka yi wa’azi sosai a kurkuku.

A lokacin da Grigoriy ya yi baftisma a 1975, bayan ya yi shekara daya yana bauta a sansanin gwamnatin Soviet don ya ki ya shiga soja. Yanzu shekarunsa 64. A shekara ta 1977, an sake shi. A shekara ta 1986 an sake kama shi an kai shi kurkuku domin an same shi da littattafanmu da aka haramta. Mahaifinsa wanda shi ma ana kiransa Ivan, ya taba zama a irin wannan sansanin daga 1944 zuwa 1950 don ya ki shiga soja.

Grigoriy ya ce: “Kasancewa da bangaskiya mai karfi tun kafin in je kurkuku ne ya taimake ni in jimre tsanantawar. Ban yi shakka ko sau daya cewa ina bin gaskiya kuma Jehobah ne Allah na gaskiya ba.”

Yanzu, dansa Ivan ma yana fuskantar irin tsanantawar nan. Grigoriy ya ce: “Na tuna abin da ya faru a lokacin da gwamnatin Soviet take mulki, kuma abin da ya faru a lokacin ne yake faruwa yanzu.” Ya kara da cewa, “Saboda haka, ina rokon Jehobah ya taimaka wa Ivan ya rike amincinsa kuma ya tsarkaka sunan Jehobah ta wurin jimre tsanantawar.”

Dan’uwa Partsey, kakan Ivan ya rasu yanzu. Amma a 1943, gwamnatin Nazi sun kai shi sansanin da ake kira Majdanek, kuma daga baya sun kai shi Ravensbrück domin ya ki saka hannu a takardar da za ta nuna cewa ya daina bauta wa Jehobah. An sake shi daga hannun sojojin Jamus, sa’ad da aka yi nasara a kan su a 1945. Amma a 1952, an sake kama shi kuma aka yanke masa hukuncin kisa. Daga baya an canja hukuncin kuma aka sake shi a 1956. Har ila an kama Dan’uwa Partsey a 1958 don imaninsa, amma aka sake shi a 1964.

Ivan ya ce: “Yadda kakana ya rike amincinsa, ya karfafa ni. A lokacin da za a ta da shi daga mutuwa, zan gaya masa cewa ni ma na fuskanci tsanantawa kamarsa kuma amincinsa ya taimaka mini in rike amincina kuma in nuna karfin zuciya.”

Ivan ya dada da cewa: “Ba wanda isa ya sa ni in daina kaunar Jehobah da yin imani da shi. Sau da yawa na gaya wa masu bincike cewa: ‘Abin da kawai za ku iya yi shi ne, ku kama ni ku sa ni a kurkuku, amma ba za ku iya sa in canja ra’ayina ba.’”

Me ya taimaka wa ’yan’uwanmu sa’ad da ake tsananta musu?

Ivan ya ce: “Ayyukan Manzanni 14:22 ya gaya mana cewa: ‘Sai tare da azaba mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.’ Wajibi ne kowane Kirista ya fuskanci jarrabawa. Ko da ba a jefa mutum a kurkuku ba, rashin lafiya ko mutuwar wani da muke kauna zai iya gwada amincinmu. Idan muna da ra’ayi mai kyau da kuma dangantaka mai kyau da Allah, za mu iya jimre kowace irin jarrabawa. A kullum, Jehobah zai taimaka wa bayinsa.”

Mahaifinsa Grigoriy ya ce: “Ka karfafa dangantakarka da Jehobah. Ka zama amininsa. Yana da muhimmanci ka tabbatar wa kanka cewa kana bin gaskiya. Hakan zai ba ka karfin yin duk wata sadaukarwa don ka ci gaba da bauta wa Jehobah. Idan ka yi hakan, Jehobah zai sāka maka.”

Hakika, yadda Jehobah ya taimaka wa ’yan’uwan da aka tsananta musu don imaninsu, abin ban karfafa ne. Za mu ci gaba da addu’a ’yan’uwanmu a Rasha su kasance da karfin zuciya kuma su rika tuna alkawarin da Jehobah ya yi cewa: “Kada ka ji tsoro,  . . . ladanka zai yi yawa sosai.”​—Farawa 15:1.