Koma ka ga abin da ke ciki

ꞌYarꞌuwa Irina Buglak

13 GA DISAMBA, 2021
RASHA

“Zama Aminiyar Jehobah Ne Yake Sa Ni Farin Ciki”

“Zama Aminiyar Jehobah Ne Yake Sa Ni Farin Ciki”

Abubuwan da Suka Faru

  1. Kotun Birnin Partizansk da ke yankin Primorye zai sanar da hukuncin da aka yanke wa ꞌYarꞌuwa Irina Buglak nan ba da dadewa ba. Wanda ya daukaka karar bai riga ya fadi irin hukuncin da yake so a yi mata ba

  2. 6 ga Agusta, 2021

    An mai da karar da aka shigar game da Irina zuwa Kotun Birnin Partizansk don a saurari karar

  3. 30 ga Nuwamba, 2020

    Da ba a sami hujjojin da za su sa a hukunta Irina ba an mai da karar ofishin wanda ya daukaka karar

  4. 31 ga Janairu, 2020

    An sake ta daga daurin talala, bayan kwana 107

  5. 16 ga Oktoba, 2019

    Bayan Irina ta yi kwana 179 a kurkuku, an sake ta amma kuma an yi mata daurin talala a gida

  6. 20 ga Afrilu, 2019

    Da karfe 3:00 na dare, jamiꞌan tsoron FSB sun zo sun bincika gidan Irina. Hukumomin sun zarge ta da shirya da kuma gudanar da taron addini. Sai aka kai ta kurkuku, inda aka kara tsawon lokacin da za ta zauna a wurin sau uku

  7. 19 ga Afrilu, 2019

    Jamiꞌan tsoron FSB guda takwas sun kai tsumame a gidan wata ꞌYarꞌuwa Nelly Tarasyuk mai shikaru 80. Irina da ꞌyarta Natalya, suna cikin ꞌyanꞌuwa matan da suke cikin gidan. Da aka kawo tsumamen, Nelly ta soma rashin lafiya kuma aka kai ta asibiti. Sauran ꞌyanꞌuwa matan kuma an kama su kuma aka soma tuhumar su da daren. Sai aka kulle Irina

Mai Ba da Labarin

Fatan mu shi ne Jehobah ya ci gaba da karfafa Irina da dukan ꞌyanꞌuwanmu da ke Rasha, su ci gaba da jimrewa da hakuri da farin ciki.​—⁠Kolosiyawa 1:⁠11.