Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA AFRILU, 2016
RASHA

Hukumomin Rasha Suna Kokarin Rufe Ofishin Shaidun Jehobah

Hukumomin Rasha Suna Kokarin Rufe Ofishin Shaidun Jehobah

ST. PETERSBURG, a Rasha​—⁠Hukumomin kasar Rasha suna barazanar rufe ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar, abin da ba a taba yi ba a tarihin Rasha.

Mai Shigar da Kara a Madadin Gwamnatin Rasha ya rubuta wata wasikar gargadi a ranar 2 ga Maris 2016, kuma a cikin wasikar ya ce, “za a dakatar da ayyukan Shaidun Jehobah” idan ofishin Shaidun Jehobah na kasar ya kasa wanke kansa daga “laifin aikata” ayyukan da gwamnati take ganin na masu “tsattsauran ra’ayi” ne. Wakilin Shaidun Jehobah na kasar rasha mai suna Yaroslav Sivulskiy ya ce: “Idan aka rufe ofishinmu na kasar, za a kwace duka dukiyoyin da kungiyarmu ta mallaka kuma za a hana mu gudanar da ayyukan ibada a kasar Rasha baki daya.”

Ofishin Shaidun Jehobah na Rasha.

Wannan matakin da kasar Rasha take kokarin daukawa ya zo ne a daidai lokacin da Shaidun Jehobah suke cika shekara 25 da samun rijista a kasar, domin an yi wa ofishin rijista ne a ranar 27 ga Maris 1991, kuma an sake masa rijistar a ranar 29 ga Afrilu 1999. Barazanar rufe ofishin Shaidun Jehobah da ke kauyen Solnechnoye, wajen kilomita 40 daga birnin St. Petersburg shi ne mataki na kwana-kwanan nan da gwamnatin kasar ta dauka a kokarinta na murkushe Shaidun Jehobah. A cikin shekarar da ta shige, gwamnatin Rasha ta dakatar da Shaidun Jehobah shigar da littattafansu da Littafi Mai Tsarki na yaren Rasha a cikin kasar. A yanzu, Rasha ce kadai kasar da ta haramta dandalin Shaidun Jehobah na jw.org. Mr. Sivulskiy ya ce: “Rasha tana amfani da dokokin da aka kafa don yaki da tsattsauran ra’ayi a hanyar da ba ta dace ba don kawai ta hana Shaidun Jehobah yin ibada.” Ya dada da cewa, “Shaidun Jehobah ba za su amince da hakan ba kuma za mu kalubalance wadannan matakan da kasar ta dauka. Muna so mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu na ibada da kuma koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a sake kamar yadda muka saba yi har tsawon shekaru 125 yanzu.”

Gwamnatin Rasha tana wulakanta Shaidun Jehobah ne don kawancen da ke tsakanin gwamnatin da Cocin Orthodox na Kasar Rasha. Kafofin yada labarai na kasashen waje, kamar, The New York Times ta ce, “kawance da ke tsakanin gwamnatin kasar da kuma Cocin Orthodox na Kasar Rasha” ne yake sa gwamnatin ta tsananta wa Shaidun Jehobah kuma ta kafa dokokin da za su iya dakatar da ayyukan Shaidun Jehobah da kuma wasu kananan addinai da ke kasar. Wani jarida mai suna The Associated Press kuma ta ce, “matakan da gwamnatin Rasha ta dauka a kan Shaidun Jehobah a kasar ya jijjiga masu gwagwarmayar neman ‘yancin gudanar da addini.” Jaridar Reuters ta ce, matakan da gwamnatin take daukawa wulakanci ne kawai da ake yi wa “Shaidun Jehobah da kuma sauran mutanen da ake zargin su da aikata laifi, duk a cikin sunan yaki da tsattsauran ra’ayi bisa ga dokar Rasha ne.” A Disamba 2015, jaridar The Independent ta ce, asali dai an kafa dokokin Rasha ne don a “kauce wa ta’addanci da kuma hukunta masu zalunci saboda kishin kasa.” Amma a yanzu, tana amfani da su wajen “hukunta masu gudanar da ayyukan ibadarsu cikin lumana.” Yadda jaridar The Huffington Post ta kwatanta Shaidun Jehobah ke nan a ranar 20 ga Maris, 2016. Shaidun Jehobah sun daukaka kara zuwa wasu kotuna a kasar Rasha da kuma Kotun Kāre Hakkin Bil-adama na Tarayyar Turai, amma a ranar 25 ga Maris, 2016, jaridar The Moscow Times ta ce, gwamnatin Rasha ta kafa wata sabuwar dokar “da ta ba kotunan Rasha damar soke duk wani hukuncin da kotunan wasu kasashe suka yanke.”

Bakin da suka kawo ziyara a ofishin Shaidun Jehobah.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha ne yake tsara aikin koya wa mutane Littafi Mai Tsarki kyauta a kasar. Dattawan da ke aiki a ofishin suna aiki da wasu Shaidun Jehobah da suke ba da kai don su iya taimaka mutanen da suke cikin bala’i. Shaidun Jehobah fiye da 175,000 ne a Rasha da ke da mutane fiye da 146,000,000.

Wani wakilin Shaidun Jehobah mai suna David A. Semonian da ke hedkwatarsu a New York ya ce: “A gaskiya ba mu ji dadin yadda gwamnatin kasar Rasha take barazanar rufe ofishinmu da ke wurin ba. Shaidun Jehobah da kuma wasu mutane a duk duniya suna jirar su ga yadda za a bi da batun.”

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, tel. +1 718 560 5000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, tel. +7 812 702 2691