22 GA YULI, 2016
RASHA
Kotu Ta Dage Zaman Sauraron Karar da Shaidun Jehobah Suka Shigar a Kan Barazanar Rufe Hedkwatarsu a Rasha Zuwa Satumba
Kotun Gunduma na Tver a kasar Rasha ta soma sauraron karar da Shaidun Jehobah suka daukaka sakamakon wasikar gargadin da Mai Shigar da Kara a Madadin Gwamnatin Kasar ya aika musu. A cikin wasikar, an yi barazanar rufe hedkwatar Shaidun Jehobah da ke kasar. Kotun ta dan saurari bangarori biyun sa’an nan ta dage zamanta zuwa ranar 23 ga Satumba, 2016. A ranar ne kotun za ta saurari bayanai dalla-dalla. Jakadun kasashe da yawa a birnin Moscow sun halarci zaman kotun.
Wasu matakan da gwamnati suka dauka a kwana-kwanan nan, barazana ne ga ‘yancin da Shaidun Jehobah suke da shi na gudanar da ayyukan ibadarsu. A ranar 20 ga Yuli, 2016 ne aka soma amfani da sabon tsarin dokar kasar wanda aka yi wa kwaskwarima, wato, Federal Law on Freedom of Conscience and on Religious Associations. A kwana a tashi, za a ga yadda hukumomin kasar Rasha za su yi amfani da wannan dokar a kan Shaidun Jehobah.