Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA MAYU, 2018
RASHA

Daukaka Kara Don Hana Hukuma Kwace Ofishin Shaidun Jehobah na Dā Da Ke Rasha

Daukaka Kara Don Hana Hukuma Kwace Ofishin Shaidun Jehobah na Dā Da Ke Rasha

A ranar Alhamis 3 ga Mayu, 2018, da karfe 11:30 na safe, kotun da ke birnin Saint Petersburg za ta saurari daukaka karar da Shaidun Jehobah suka yi game da hukuncin da aka yanke a watan Disamba 2017. Wannan hukunci da aka yanke zai ba hukumar kasar Rasha damar kwace ginin ofishinmu na dā a Rasha. Idan kotu ta ki amincewa da daukaka karar da muka yi, hukuma za ta kwace gidajen 14 ba tare da bata lokaci ba.