Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA AFRILU, 2016
RASHA

An Shigar da Wasu Kararraki a Kwanan Nan don Ana Neman a Takura wa Shaidun Jehobah a Rasha

An Shigar da Wasu Kararraki a Kwanan Nan don Ana Neman a Takura wa Shaidun Jehobah a Rasha
  • Yankin Taganrog, Rostov. A ranar 17 ga Maris, 2016, Kotun Yanki na Rostov ya goyi bayan hukuncin da wani karamin kotu ya yanke na kama Shaidun Jehobah guda 16 da laifin yin ibada, amma ya rage tarar da aka ci mutane 12 daga cikinsu zuwa dala 147. Kari ga haka, ya dakatar da zartar da wannan hukuncin, amma ba a san manufar hakan ko kuma dalilin da ya sa ya rage tarar ba.

  • Wani lauya mai shigar da kara yana neman ya saka Littafi Mai Tsarki a cikin jerin “littattafai da suke koyar da tsattsauran ra’ayi.” Wani lauyan da ya shigar da kara a madadin Leningrad-Finlyandskiy Transport yana nema a ba shi dama don ya saka juyin New World Translation of the Holy Scriptures da Shaidun Jehobah suka buga, a cikin jerin “littattafai da suke koyar da tsattsauran ra’ayi.” Hakan ya saba wa sashen dokar kasar da ke yaki da tsattsauran ra’ayi, wato, Article 3-1 na Federal Law on Counteracting Extremist Activity. Wannan dokar ta hana saka Littafi Mai Tsarki a cikin jerin littattafai da ke koyar da tsattsauran ra’ayi. Ko da yake juyin New World Translation Littafi Mai Tsarki ne, wannan lauyan ya ce juyin da aka fitar bisa ga “al’adu masu tsarki” na Cocin Orthodox na Rasha ne kadai suka cancanci a kira su Littafi Mai Tsarki. Kotun Birnin Vyborg zai sake sauraron karar a ranar 26 ga Afrilu, 2016.