Koma ka ga abin da ke ciki

YUNI 28, 2017
RASHA

Kotu Ya Ki Ba da Izini A Saki Dennis Christensen

Kotu Ya Ki Ba da Izini A Saki Dennis Christensen

A ranar 21 ga Yuni 2017, Kotun Yanki da ke Oryol ya ki saurarar karar da Dennis Christensen ya shigar don kulle shi da aka yi. Malam Christensen dan kabilar Danish ne. Jami’an tsaro na Federal Security Service (FSB) sun kai wa Shaidun Jehobah hari babu zato kuma suka kama Malam Christensen don yana ayyukan ibada na Shaidun Jehobah.

Kwana-kwanan nan ne Kotun Koli na kasar Rasha ya yanke hukuncin cewa Shaidun Jehobah masu tsattsaurar ra’ayi ne kuma ya dakatar da ayyukan da suke yi a kasar. Jami’an tsaro da suka kai wa Shaidun hari a ranar sun ce za a ci Shaidun Jehobah tara don sun ci gaba da yin ayyukan da aka haramta a kasar. Jami’an tsaron sun nemi kotu ya ba su izini su ci gaba da tsare Malam Christensen har sai ranar 23 ga Yuli, 2017. Ko da yake ba shi da laifi kuma shi mutum ne mai son zaman lafiya, amma hukumar ta yi hakan ne don ta nemi hujjojin da za su sa a same shi da laifi.

Shaidun Jehobah suna kan neman alfarma daga kotun kuma suna yin shiri don su kāre ’yancin da suke da shi na yin ibadarsu, kamar yadda dokar kasar da kuma Rukunin Turai na ‘Yancin ‘Yan Adam suka amince da shi.