Koma ka ga abin da ke ciki

23 GA NUWAMBA, 2017
RASHA

Kotun Rasha za ta saurari daukaka kara domin an kira Littafi Mai Tsarki littafin tsattsauran ra’ayi

Kotun Rasha za ta saurari daukaka kara domin an kira Littafi Mai Tsarki littafin tsattsauran ra’ayi

A ranar 6 ga Disamba, 2017, Kotun Leningrad za ta saurari daukaka karar da Shaidun Jehobah suka yi domin wata karamar kotu ta hana yin amfani da fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Rasha.

A watan Agusta 2017, Kotun da ke birnin Vyborg ta amince da abin da lauya mai gabatar da kara ya ce. Lauyan ya ce juyin New World Translation ba Littafi Mai Tsarki ba ne domin an yi amfani da “Jehovah” a matsayin baƙaƙe hudu da suke wakiltar sunan Allah. Amma lauyan ya taka doka domin dokar kasar ta hana mutum kiran Littafi Mai Tsarki littafin ayyukan tsattsauran ra’ayi don.

Shaidun Jehobah wadanda su ne suka wallafa Littafi Mai Tsarki juyin New World Translation a yaren Rasha sun ki amincewa da hukuncin da kotun da ke birnin Vyborg ta yanke cewa juyin Littafin an yi sa ne don tsattsauran ra’ayi. Juyin Littafi Mai Tsarki na New World Translation juyin ne da aka buga sashe ko kuma gabaki daya a yaruka 161, ban da haka, ana daraja wannan juyin don babu kuskure kuma yana da sauƙin karantawa. Kuma an rarraba kofi fiye da miliyan 200.