19 GA AFRILU, 2017
RASHA
Rana Ta Biyar Da Kotun Koli Ta Rasha Ke Shari’a: An Sake Bincike Kalubalen Da Shaidun Jehobah Suka Fuskanta Cikin Shekara Goma Da Suka Shige
NEW YORK—A ranar Laraba 19 ga Afrilu, 2017, mutane 300 ne suka zo (wasu ma da karfe 2:00 na safiya suke wurin) domin su saurari kara a rana ta biyar da Gwamnatin Rasha ta shigar Kotun Koli. Dalilin hakan shi ne cewa tana so a rufe Ofishin Shaidun Jehobah. Hukumomin Rasha sun dau tsawon shekaru goma suna zaluntar Shaidun Jehobah. Kotu ta takaita hakan yanayi da ta bincika Takardu 43 da aka gabatar a gaban ta.
A lokacin da ake shari’ar, lauyan Gwamnatin bai iya ba da kwakkwarar dalilin da ya sa suke so a rufe Ofishin Shaidun Jehobah ba. Kari ga haka, bai bayyana wani abin da mutanen da suke aiki a Ofishin ko kuma Shaidun Jehobah a kasar suka yi da ya nuna cewa su ‘yan tsattsaurar ra’ayi ne ba. Daya daga cikin lauyoyin Ofishin Shaidun Jehobah mai suna Yury Toporov ya nuna wa Kotun lambobin yabo da takardun yabo da gwamnati ta ba Ofishin Shaidun Jehobah don kyawawan ayyukan da suke yi wa jama’a a kasar. Ya kuma tuna masu da irin ayyuka masu kyau da ikilisiyoyin Shaidun Jehobah suka yi da ya taimaka wa jama’a a yankinsu. Kari ga haka, wani lauyan gwamnati ya amince cewa bayan Gwamnatin ta bincike duk takardun da Shaidun Jehobah na kasar Rasha ke amfani da su tun 2008 ba ta sami su da wani halin tsattsaurar ra’ayi ba.
Kotun za ta sake saurara karar 20 ga Afrilu, 2017 da karfe 2:00 na rana.
Media Contacts:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000
Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-911-087-8009