Koma ka ga abin da ke ciki

20 GA AFRILU, 2017
RASHA

Kotun Kolin Rasha Ta Hana Shaidun Jehobah Yin Ayyukan Ibadarsu

Kotun Kolin Rasha Ta Hana Shaidun Jehobah Yin Ayyukan Ibadarsu

NEW YORK​—⁠Bayan Kotun Kolin Rasha ta yi sati biyu yana saurarar karar da aka shigar a kan Shaidun Jehobah, kotun ta yanke hukunci cewa a rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha da kuma wuraren ibadarsu 395. Za a soma hakan nan da nan.

Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna Yaroslav Sivulskiy ya ce, “Wannan hukuncin ya sa mu bakin ciki kwarai da gaske kuma mun damu da yadda hakan zai shafi ayyukan ibadarmu a kasar Rasha. Za mu daukaka karar nan kuma muna fatan cewa za a kwato mana hakkinmu kuma a mayar mana da ‘yancinmu da yin addininmu cikin lumana.”

An ba Shaidun Jehobah kwana 30 don su daukaka karar don lauyoyi uku su sake duba al’amarin.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-911-087-8009