16 GA YUNI 16, 2017
RASHA
Hukuncin da Kotun Kolin Rasha Ta Yanke wa Shaidun Jehobah Ya Sa Ana Take Hakkinsu
Hukuncin da kotun Kolin ta yanke wa Shaidun Jehobah a ranar 20 ga Afrilu 2017, ya yi masu mummunar illa a kasar gabaki daya. Hukumar na taka ’yancin Shaidun Jehobah kuma ta haramta su daga yin ayyukan ibadarsu. Har ila, wasu ’yan kasar Rasha sun ce wannan hukuncin ya sa mutane suna nuna wa Shaidun Jehobah bambanci da kuma wulakanta su.
Gwamnatin Rasha Tana Wulakanta da Kuma Taka Dokar ’Yancin Dan Adam
Tuhumar da Aka Yi wa Shaidun Jehobah
A ranar 25 ga Mayu, ’yan sanda sun kai wa Shaidun Jehobah hari a ikilisiyar Oryol sa’ad da suke taron ibada. ’Yan sanda sun kama Dennies Christensen wani dan kasar Denmak da dattijo ne a ikilisiyar Oryol. Malam Christensen yana nan a tsare, yana zaman jiran shari’a da za a masa a ranar 23 ga Yuli kuma mai shari’a yana neman hanyoyin tuhumar sa da laifin “tsattsauran ra’ayi.” In shari’ar ta ka da shi, Malam Christensen zai yi shekara shida zuwa goma a kurkuku.
Gwamnati Ta Yi wa Shaidun Jehobah Kashedi
A ranar 4 ga Mayu, Ofishin mai shari’a ta mika wasikar kashedi wa mai kujerar ikilisiyar. Wasikar kashedin ya ambata cewa shi mai kujerar da mambobin ikilisiyar za su fuskanci tuhuma daga hukuma idan har suna halartar taron ibada.
Tun lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci, an ba wa akalla ikilisiyoyi biyar wannan kashedin.
’Yan Sanda Sun Kai wa Wurin Taron Ibada Hari
A ranar 22 ga Afrilu, ’yan sanda a Dzhankoy, Jamhuriyar Crimea sun shiga gidan ibada na Shaidun Jehobah yayin da suke kammala taronsu. ’Yan sandan sun ce bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, Shaidun Jehobah ba su da izinin su yi taron ibada. Sun bincika ginin kuma suka rufe wurin domin kada a sake halartar taron ibada a wurin.
Tun lokacin da Kotun Koli ta yanke hukuncin, ’yan sanda sun katse taron ibada na Shaidun Jehobah akalla so biyu, daya daga cikinsu shi ne wanda aka yi a gidan wani Mashaidin.
Michael Georg Link, Darektan OSCE na Office for Democratic Institutions and Human Rights ya ce: “Na damu kwarai da yadda ake cin zali da kuma haramta ayyukan Shaidun Jehobah a Rasha. . . . Bisa ga farillar kasar a karkashin doka ta ’yancin dan Adam a duk fadin duniya da kuma alkawarin OSCE [Organization for Security and Cooperation in Europe],” ina rokan Gwamnatin Rasha da ta kare ’yancin Shaidun Jehobah, ta bar su su ci gaban da bin addininsu, ta ba su ’yancin yin taro da kuma ayyukan ibadarsu.
An Yi Fakon ’Ya’yan Shaidun Jehobah da Ke Makarantu
A ranar 24 ga Afrilu, a kauyen Bezvodnoye da ke yankin Kirov, wata malaman makaranta ta wulakanta wasu yara dalibai wanda mahaifiyarsu Mashaidiya ce. Malamar ta ce ta yi hakan ne domin an saka wa Shaidun Jehobah takunkumi a Rasha.
ranar 17 ga Mayu, a yankin Mosco, wani shugaban makaranta ya rubuta kashedi wa iyayen wani dan dalibi mai shekara takwas wanda ya yi wa abokansa wa’azi. Takardar ta yi magana a kan shawarar da Kotun Koli ta tsai da game da yadda ta hana “kowace irin ayyuka da ba ta shafi harkokin makaranta ba.” Shugaban makarantar ya yi barazanar kai kara wa ’yan sanda sa’an nan kuma ya sa “a tura yaron zuwa wata makaranta dabam don a horar da shi yadda ya dace.”
An Hana wa Maza da Shaidun Jehobah Ne Gatar Hidimar Farin Hula
A ranar 28 ga Afrilu, hukumar da aka nada don tilasta yin aikin soja na yankin Cheboksary da Marposdskiy, ta ki karban wasikar da suka kawo na neman wata aiki wanda yake dabam da na soja. Hukumar ta ce Shaidun Jehobah masu tsattsauran ra’ayi ne kuma ba su cancanci a ba su wani aiki dabam ba.
Maza akalla biyu wanda su ma Shaidun Jehobah ne, an ki karban wasikunsu na neman wani aikin farin hula.
Phillip Brumley, lauyan Shaidun Jehobah ya gano wata rashin gaskiyar gwamnati. Ya ce: “Gwamnati ta ki ba wa matasan Shaidun Jehobah gatar daukan wani aiki dabam domin wai su masu tsattsauran ra’ayi ne. Har ila kuma, gwamnatin tana tilasta wa wadannan mutanen da ta ce su masu “tsattsauran ra’ayi” ne da su shiga aikin soja. Shin akwai wata hikima a ciki da za a ce wa masu “tsattsauran ra’ayi su shiga aikin soja?”
Wulakanci da Nuna Wariya
Cin Zalin da Ake wa Shaidun Jehobah
A ranar 30 ga Afrilu, a Lustino da ke yankin Moscow, an kone gidan wani iyali da Shaidun Jehobah ne hade da gidan iyayensu tsofaffi. Kafin mutumin ya saka wutar, ya fadin yadda ya ki jinin addinin iyali nan.
A ranar 24 ga Mayu, a Zhesthart da ke Jamhuriyar Komi, wasu mutane sun yi mummunar barna a inda Shaidun Jehobah suke ibada.
An lalata wuraren ibada akalla guda tara tun lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci a ranar 20 ga Afrilu 2017.
A ranar 26 ga Afrilu, wani Mashaidin Jehobah a Belgorod na barin gidansa ke nan, sai wani ya yi masa ihu ya ce, “Doka ta hana aikinku!” sai ya yi masa duka.
A ranar 11 ga Mayu, wasu mutane sun je sun katse taron Shaidun Jehobah a Tyumen kuma suka ta yin bakar maganganu da kazamin kalamai kuma suka yi barazanar cewa za su ji ma wadanda suka halarci taron rauni.
An Kori Shaidun Jehobah Daga Wurin Aiki
A ranar 15 ga Mayu, an kori duk ma’aikata Shaidun Jehobah a wani kamfani a Dorobozh da ke yankin Smolensk. Manyan ma’aikatan kamfanin sun ce FSB ce ta ba su umurni da su kori duk wani Mashaidin Jehobah domin wai su “masu tsattsauran ra’ayi” ne. Don haka ba su cancanci su yi aiki a kamfanin ba.
Shaidun Jehobah sun fuskanci barazanar kora daga aiki. Hakan ya faru akalla so uku tun lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci cewa su masu tsattsauran ra’ayi. A kauyen Yashkino da ke yankin Kemerovo, ’yan sanda sun matsa ma wata Mashaidiya, amma ta ki ta ba da bayanai game da sauran Shaidun Jehobah. ’Yan sandan sun ce ketare doka ne a yi tarayya da addinin da aka hana kuma aka kwatanta Shaidun Jehobah da ’yan ta’addan ISIS.
An Damu da Lafiyar Shaidun Jehobah a Rasha
Shekaru goma kafin Kotun Koli ta yanke hukunci, gwamnati na biyan wasu mutane su dinga tsananta wa Shaidun Jehobah a Rasha saboda da addininsu. A yanzu da kotun ta yanke hukunci, lamarin ya kara muni sosai. Wannan hukuncin ya sa Shaidun Jehobah sun rasa darajarsu kuma ya ba wa mutane da kuma ma’aikatan gwamnati karfin gwiwar kara tozarta su, kamar yadda kuka ganin a abubuwan da suka faru kwana-kwanan nan. Shaidun Jehobah a fadin duniya sun damu ainun game da abin da zai faru da ’yan’uwansu a Rasha idan Kotun Koli ta amince da hukuncin nan da aka yanke. Kotun za ta saurari karar a ranar 17 ga Yuli 2017.
Malam Brumley ya ce: “Babu wanda ya iya ba da kwakkwarar hujjar da ta nuna cewa Shaidun Jehobah masu tsattsauran ra’ayi ne. Irin zargin da ake tuhumar Shaidun Jehobah da shi bai kai rabin mummunar tsanantawar da ake masu ba. Ya kamata Gwamnatin Rasha ta sake tunani a kan hukuncin da ta yanke wa Shaidun Jehobah bisa ga nasu dokoki da kuma yarjejeniyar da suka yi game da ’yancin bin addini.”