Koma ka ga abin da ke ciki

26 GA YUNI, 2017
RASHA

Ma’aikatan Gwamnatin Rasha Sun Yaba wa Shaidun Jehobah Har da Wani Dan Denmark da Ke Kurkuku Don Saka Hannu Wajen Tsabtace Mahalli

Ma’aikatan Gwamnatin Rasha Sun Yaba wa Shaidun Jehobah Har da Wani Dan Denmark da Ke Kurkuku Don Saka Hannu Wajen Tsabtace Mahalli

Wasika daga ma’aikatan gwamnatin Oryol: “Muna godiya don ayyuka masu kyau da ku ka yi don taimakon jama’a da kuma mahalli.”

NEW YORK​—A ranar 2 ga Yuni 2017, ma’aikatan gwamnatin birnin Oryol sun yaba wa wani ikilisiyar Shaidun Jehobah don taimakon da suka yi a ranar 22 ga Afrilu, 2017, wajen tsabtace mahallin da ake yi kowace shekara. Shaidun Jehobah 70 ne suka ba da kansu a ranar wajen share datti da ke kan titin Oryol da kuma dattin Kogin Orlik da ya wuce cikin birnin. Ma’aikatan gwamnatin sun nuna godiyarsu ta wurin ba Shaidun wata ƙaramar kyauta da kuma wasiƙa da ta ce: “Muna godiya don ayyuka masu kyau da ku ka yi don taimakon jama’a da kuma mahalli.”

Amma bayan wata ɗaya da tsabtace mahallin da suka yi, sati daya kafin ma’aikatan su nuna wa Shaidun Jehobah godiyarsu, an kama Dennis Christensen, wani Mashaidi a taronsu na ibada a ranar 25 ga Mayu (hotonsa ne a sama), wai yana daukaka tsattsaurar ra’ayi. Hukumomin Rasha suna zargin Shaidun Jehobah cewa su masu tsattsaurar ra’ayi ne, kuma suna amfani da hakan don su kai masu hari a kasar.

Dennis Christensen yana taimakawa wajen tsabtace mahalli a watan Oktoba 2011.

David A. Semonian, kakakin Shaidun Jehobah a hedkwatarsu ya ce: “Mutanen da suka san Shaidun Jehobah ba su yi mamaki cewa Dennis da kuma wasu mambobinsu sun ba da kai don tsabtace mahalli ba. Sun dade suna yin hakan har ma da lokacin da aka kwace ofishinsu a shekara ta 2016. An san Shaidun Jehobah a Oryol da kuma wasu kasashe a fadin duniya da cewa su masu bin doka ne sosai. Shi ya sa abin ya ba da mamaki yadda hukuma ta yi wa Dennis, domin shi Kirista mai bin doka ne, amma sun dauke shi dan ta’adda bayan taimakon da ya yi a tsabtace mahalli kuma ma’aikatan gwamnatin Oryol sun ji dadin aikin da ya yi. Ya kamata a saki Dennis nan da nan kuma a bar shi ya ci gaba da yin ibadarsa da kuma taimaka wa al’umma tare da ‘yan’uwansa.”

An kama Malam Christensen bayan an yi shekara daya da aka rufe ofishin Shaidun Jehobah da ke Oryol a ranar 14 ga Yuni, 2016. An yanke wa Mallam Christensen hukunci a ranar 20 ga Afrilu, 2017, a ranar ne Babban Kotun Rasha ta tsai da shawarar kwace Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha kusa da St Petersburg. Har yanzu ba a yanke wa Malam Christensen shari’a ba, yana tsare a Oryol.

Inda Aka Samo Labarin:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000