2 GA AGUSTA, 2017
RASHA
Mutane A Fadin Duniya Sun Yi Magana Game da Hukuncin da Kotun Kolin Rasha Ya Yanke wa Shaidun Jehobah
Hukumomi da kuma ma’aikatan gwamnati a fadin duniya sun fadi ra’ayinsu game da hukuncin da Kotun Koli na Rasha ya yanke wa Shaidun Jehobah kuma ya hana su yin ayyukansu na ibada. Abubuwan da suka fada sun nuna cewa kasar Rasha ba ta yi wa Shaidun Jehobah masu son zaman lafiya adalci ba.
A ranar 17 ga Yuli ga 2017, wasu lauyoyi guda uku na Kotun Kolin Rasha sun sake karfafa hukuncin da kotun ta yanke a ranar 20 ga Afrilu. Hukuncin ta ce a “rufe ofishin Shaidun Jehobah a Rasha kuma a kwace duka wuraren ibadar Shaidun Jehobah a kuma mika su ga Hukumar Rasha.” Wannan hukuncin na nufin cewa kotun ta hana Shaidun Jehobah daga yin ayyukan ibadarsu a Rasha.
Abubuwan da Suka Fada Bayan da Aka Yanke Hukunci a Ranar 17 ga Yuli, 2017
Bayanin da ke gaba, maganganu ne da wasu mutane suka yi a ranar 17 ga Yuli, 2017, bayan lauyoyin Kotun Koli na Rasha sun karfafa hukuncin da aka yi a ranar 20 ga Afrilu:
Wani babban Minista da ke Britaniya mai suna Lord Ahmad of Wimbledon ya ce: “Mun damu sosai don yadda Kotun Koli na Rasha ya ki saurarar karar da Shaidun Jehobah suka shigar kuma ya ce su masu ‘tsattsaurar’ ra’ayi ne. Wannan hukuncin na nufin cewa za a bi da Shaidun Jehobah guda 175,000 da ke Rasha kamar ’yan ta’ada kuma a hana su ’yancin bin addininsu kamar yadda dokar Rasha ta tanadar.” https://www.gov.uk/government/news/minister-for-human-rights-statement-on-russian-supreme-court-ruling
Wani wakilin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amirka, wato U.S. Department of State mai suna Heather Nauert ya ce: “Hukuncin da Kotun Kolin Rasha ya yanke wa Shaidun Jehobah wannan makon ya nuna irin tsanantawar da Rasha suke wa masu bin addini. Muna rokon hukumomin Rasha da su daina hana Shaidun Jehobah yin ayyukan ibadarsu, su sa kada a rufe ofishin Shaidun Jehobah, kuma su saki Shaidun Jehobah da suka kama.” https://www.state.gov/r/pa/prs/ps/2017/07/272679.htm
Wani wakilin Ministocin Harkokin Waje na Tarayyar Turai, wato European Union External Action Services ya ce: “Ya kamata a bar Shaidun Jehobah su yi ibadarsu a cikin kwanciyar hankali kamar yadda sauran addinai suke yi. Domin haka Constitution of the Russian Federation da kuma Russia’s international commitments and international human rights standards ta ce a yi.” https://eeas.europa.eu/headquarters/headquarters-homepage/30022/statement-spokesperson-upheld-ban-activities-jehovahs-witnesses-russia_en
Wani Shugaban Kungiyar da ke kāre ’yancin addini, wato United States Commission on International Religious Freedom mai suna Daniel Mark ya ce: “Hukuncin da Kotun Kolin ya yanke ya nuna cewa gwamnatin suna yin alaka da masu bin addini da kuma masu tsattsaurar ra’ayi. Shaidun Jehobah ba masu tsattsaurar ra’ayi ba ne don haka, wajibi ne a bar su su yi ayyukan ibadarsu ba tare da matsi daga gwamnati ba.” http://www.uscirf.gov/news-room/press-releases/russia-jehovah-s-witnesses-banned-after-supreme-court-rejects-appeals
Shugaban Intersocietal Cooperation With Russia, Central Asia, and the Eastern Partnership Countries, Foreign Ministry of Germany mai suna Gernot Erler ya ce: “Na damu sosai da na ji cewa kotun ya hana ayyukan Shaidun Jehobah a Rasha. Duk da roke-roken da muke yi, sun ki barin su su yi addininsu cikin kwanciyar hankali kuma hakan laifi ne babba.” http://www.auswaertiges-amt.de/sid_5DAC942B7DE50BCC4AFCDFC864C2E383/EN/Infoservice/Presse/Meldungen/2017/170719-Ko_RUS-Zeugen_Jehovas.html
Shugaban Kungiyar Lantos Foundation mai suna Dr. Katrina Lantos Swett ta ce: “A gaskiya, hukuncin da kotun Rasha ya yanke na hana Shaidun Jehobah yin ibadarsu a Rasha cin zalin ne kuma sun taka ’yancin bin addini da kowa yake da shi kamar yadda Talifi na 18 na Universal Declaration of Human Rights ya ce. . . . Ya kamata duk masu addini da kuma wadanda suke daraja ’yancin kai su goyi bayan Shaidun Jehobah da ke Rasha.” https://www.lantosfoundation.org/news/2017/7/17/lantos-foundation-condemns-russias-outrageous-decision-to-ban-jehovahs-witnesses
Abubuwan da Suka Fada Bayan da Aka Yanke Hukuncin a Ranar 20 ga Afrilu, 2017
Kafin wasu lauyoyi su sake jin karar da aka shigar, ma’aikatan gwamnati da yawa sun yi magana game da hukuncin da Kotun Kolin Rasha ya yanke a ranar 20 ga Afrilu:
Sa’ad da wata Shugaba mai suna Angela Merkel take wani taron manema labarai tare da Shugaba Putin, ta ce: “Na gaya wa Shugaba Vladimir Putin da ya yi amfani da ikon da yake da shi ya kwato ’yancin mutane a nan har da Shaidun Jehobah.” http://uk.reuters.com/article/uk-russia-germany-putin-syria-idUKKBN17Y1JZ
Wasu ma’aikata a PACE Monitoring Committee for the Russian Federation masu suna Theodora Bakoyannis da Liliane Maury Pasquier sun ce: “Kotun Kolin Rasha ya ce Shaidun Jehobah kungiyar masu tsattsaurar ra’ayin ce kuma ya yanke hukunci cewa a rufe Ofishinsu da ke Rasha da kuma Majami’ar Mulkin Shaidun Jehobah guda 395. Wannan ba karamar magana ba ce domin yana nufin cewa mutum ba shi da ’yancin bin addinin da yake so a Rasha. Kuma kotun ya taka dokar da ta kyale masu tsattsaurar ra’ayi ’yancin yin magana a kotun ko a gaban jama’a.” http://assembly.coe.int/nw/xml/News/News-View-EN.asp?newsid=6599
Shugaban Kungiyar Tsaro da Hadin Kan Turai mai suna Sanata Roger Wicker ya ce: “Tun da Rasha ba ta daraja ’yancin dan Adam na bin addini, hakan ya nuna cewa ba ta cika alkawarinta ga kungiyar OSCE [Kungiyar Tsaro da Kuma Hadin Kai Na Turai] ba. Bai kamata a ci zalin mutanen da suke yin addininsu cikin kwanciyar hankali ko a saka su cikin kurkuku ko kuma a ci musu tara ba. Kuma da kotun ya ce a kwace duka abubuwan da Shaidun Jehobah suka da shi cin mutunci ne sosai. Ina fatan cewa Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam zai sake saurarar wannan karar kuma ya yi adalci.” http://csce.emailnewsletter.us/mail/util.cfm?gpiv=2100141660.2454.614
Wani wakilin Ministocin Harkokin Waje na Tarayyar Turai ya ce: “Hukuncin da Kotun Kolin Rasha ya yanke jiya cewa a hana duk ayyukan da ake yi a ofishin Shaidun Jehobah a Rasha saboda ana ganin su masu tsattsaurar ra’ayin ne zai iya sa a cin zalin Shaidun sosai don kawai suna bauta wa Allah. Wajibi ne a kyale Shaidun Jehobah su yi addininsu cikin salama kamar yadda sauran addinai suke yi bisa ga abin da Constitution of the Russian Federation da kuma Russia’s international commitments and international human rights standards ya ce.” https://eeas.europa.eu/headquarters/headquarters-homepage/24870/statement-ban-activities-jeho
Wani darektan OSCE Office for Democratic Institutions and Human Rights mai suna Michael Georg Link ya ce: “Gaskiya na damu sosai da wannan hukuncin da aka yanke wa Shaidun Jehobah a Rasha, kuma hakan zai hana su samu ci gaba a kasar. Hukuncin da Kotun Kolin ya yanke yana bata dokokin gwamati da mutane suka dogara a kai.” http://www.osce.org/odihr/313561
Wani Farfesa mai suna Ingeborg Gabriel da ke wakiltar Shugaban Kungiyar OSCE wanda ke Yaki da Nuna Kiyayya da Kuma Wariyar Launin Fata ya ce: “Wannan hukuncin da aka yanke da ya hana mutanen nan masu son zaman lafiya yin ibadarsu ya keta dokar da aka kafa a fadin duniya da kuma Kundun Tsarin Mulkin Kasar game da ’yancin bin addini. Don haka, kotun yana bukatar ya canja hukuncinsa nan da nan.” http://www.osce.org/odihr/313561
Wata Ministar Harkokin Waje na Kasashen Renon Birtaniya da Majalisar Dinkin duniya (Minister of State for the Commonwealth and the UN at the Foreign and Commonwealth) mai suna Baroness Joyce Anelay ta ce: “Na yi mamaki da Kotun Kolin Rasha ta ce Shaidun Jehobah masu tsattsaurar ra’ayi ne. Wannan hukuncin na nufin cewa za a bi da Shaidun Jehobah guda 175,000 da ke Rasha kamar ’yan ta’ada kuma a hana su ’yancin bin addininsu duk da cewa dokar kasar ta ba wa kowa ’yanci bin addinin da yake so. Gwamnatin Amirka ta ce wa gwamnatin Rasha da ta cika alkawarinta game da ’yancin dan Adam.” https://www.gov.uk/government/news/minister-for-human-rights-criticises-russian-supreme-court-ruling-for-labelling-jehovahs-witnesses-as-extremist
Hukumomi a Fadin Duniya Sun Yi Allah Wadai a Kan Hukuncin da Kotun Kolin Rasha Ta Yanke
A ranar 20 ga Yuli 2017, Permanent Council na Kungiyar OSCE ta karbi wasika daga Tarayyar Turai (EU). Wasikar ta ce wa gwamnatin Rasha da ta kyale Shaidun Jehobah su “ci gaba da yin ayyukan ibadarsu ba tare da matsi ba kamar yadda Kundun Tsarin Mulkin Kasar ya fada da kuma Russia’s international commitments and international human rights standards ta tanadar.” An rubuta wasikar a babban birnin Vienna, kuma kasashe 28 na Turai da kuma Ostareliya da Kanada da Norway sun amince da hakan. https://eeas.europa.eu/sites/eeas/files/pc_1155_eu_jehovahs_witnesses_in_russia.pdf
Shaidun Jehobah sun yi bakin ciki sosai don hukuncin da Kotun Kolin Rasha ta yanke kuma ta hana su yin ibadarsu a kasar. Abubuwan da wadannan hukumomi da ma’aikata a fadin duniya suka ce ya nuna cewa Gwamnatin Rasha ba ta yi adalci ba da ta ce Shaidun Jehobah masu tsattsaurar ra’ayi ne kuma ta ki bin dokar kasarta na kare ’yancin bin addini. Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam zai sake saurari wannan karar kuma muna fatan zai sa a canja hukuncin da aka yanke musu.