Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA AFRILU, 2017
RASHA

Kotun Kolin Rasha Ya Sake Sauraron Kara A Rana Ta Hudu

Kotun Kolin Rasha Ya Sake Sauraron Kara A Rana Ta Hudu

NEW YORK​—Mutane da yawa sun halarci Kotun Koli a rana ta huɗu da kotun zai saurari karar da Gwamnati ta shigar a kan Shaidun Jehobah na cewa a rufe Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha. A ranar da yamma, sai Kotun ta sake daga karar zuwa ranar Laraba 19 ga Afrilu 2017 da karfe 10:00 na safe.

Lauyan Shaidun Jehobah ne ya fara gabatarwarsa kuma ya bayyana cewa rashin adalci ne in aka rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha. Bayan haka, sai lauyoyin Gwamnatin suka ba da nasu gabatarwar. Da alkalin ya saurari gabatarwar da lauyan Shaidun Jehobah ya yi, sai ya bukaci lauyoyin Gwamnatin kasar su ba da hujjojin da ya sa suke so a rufe Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha. Lauyoyin ba su iya nuna wani shaida ko kuma amsa tambayoyin da alkalin ya yi musu ba. Bayan kotun ta gama saurarar dukan gabatarwar lauyoyin, sai ta daga karar.

A mako na gaba, kotun za ta sake bincike karar da aka shigar.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-911-087-8009