5, GA DISAMBA, 2017
RASHA
Sauraron Yankan Shari’a Akan Kwatar Ofishin Shaidun Jehobah ta Rasha
Gwamnatin Rasha na ci gaba da daukan matakan kwace Ofishin Shaidun Jehobah da ke Solnechnoye kusa da birnin St. Petersburg.
A ranar 20 ga Afrilu, 2017, kotu a kasar Rasha ta ba da umurni a rufe duk wuraren ibada na Shaidun Jehobah, har ma da ofishinsu da ke kasar. Duk da cewa ginin ofishin na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania (WTPA) da ke Amirka ne. Lauyan gwamnatin na son ya bata yarjejeniyar da ka yi tun shekaru 17 cewa ginin na WTPA ne wato Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. Ba a taba shakka ko WTPA ce take da wannan ginin ba, har sai da gwamnatin Rasha ta shigar da kara kotun koli, kuma WTPA ce ke biyan haraji tun lokacin da aka yi yarjejeniya cewa ginin nasu ne. Gwamnatin kasar ta kwace ginin daga wurin daga wurin Shaidun Jehobah.
A ranar 29 ga Nuwamba 2017, wato lokacin saurar karar, alkalin ya ki saurarar lauyan Shaidun Jehobah domin lauyan gwamnatin Rasha ya sami daman cin gaba. Wannan gini da gwamnati ta kwace, gini ne mai sada sosai da ya kai miliyoyin dala. Ban da haka, wannan ginin wuri ne da ’yan Rasha kusan 400 da kuma wasu daga kasashe dabam-dabam suke zama, wasun su ma sun yi fiye da shekaru 20 suna zama a wurin. Barin gidajensu da kuma hana su hidima ga ’yan’uwansu a Rasha yana damun su sosai.
A ranar 7 ga Disamba, 2017 da karfe 2 na rana ne za a kara saurarar karar a Kotun da ke St. Petersburg.