Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA AFRILU, 2017
RASHA

Shaidun Jehobah Sun Ba da Nasu Shaidar a Rana ta Uku na Sauraron Shari’a a Kotun Kolin Rasha

Shaidun Jehobah Sun Ba da Nasu Shaidar a Rana ta Uku na Sauraron Shari’a a Kotun Kolin Rasha

NEW YORK​—A rana ta uku kafin Kotun Koli na Rasha ya yanke hukunci, kotun ya sanar da cewa zai je hutu sai ranar Laraba, 12 ga Afrilu, 2017 da karfe 10 na safe kafin ya ci gaba da sauraron karar. Yau kotun ya ba Shaidun Jehobah hudu damar gabatar da shaidarsu, kuma Shaidun sun kalubalanci Ma’aikatar Shari’a na Rasha da ke yunkurin rufe ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar da kuma hana ayyukansu.

Alkalin ya yi wa Ma’aikatar Shari’ar tambayoyi da yawa kuma ya bukace su su ba da hujjojin da suka nuna cewa Shaidun Jehobah masu tsattsauran ra’ayi ne kuma suna rarraba littattafan da ke koyar da tsattsauran ra’ayi. Ma’aikatar Shari’ar ta kasa tanadar da wata hujjar da ke goyon bayan zargin da suke yi wa Shaidun Jehobah. Vasiliy Kalin, daya daga cikin kwamitin da ke kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha ya ce wa Kotun: “Ina so in tuna wa Ma’aikatar Shari’a na Rasha cewa, sa takunkumi a kan Shaidun Jehobah da take yunkurin yi zai takura wa mutanen da suke son su da zaman lafiya ne.”

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-911-087-8009