Koma ka ga abin da ke ciki

8 GA YUNI, 2017
RASHA

Shugaban Rasha Ya Ba da Lambar Yabo ga Shaidun Jehobah

Shugaban Rasha Ya Ba da Lambar Yabo ga Shaidun Jehobah

NEW YORK​—⁠A ranar 31 ga Mayu, 2017, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba wasu Shaidun Jehobah masu suna Valeriy da Tatiana Novik lambar yabo da ake kira “Parental Glory” (Daukaka ga Iyaye),a lokacin wani biki da aka yi a Kremlin a kasar Moscow. Suna zama a Karelia kuma yaransu takwas.

An yi bikin a Kremlin a jajibirin International Children’s Day (Bikin Yara na Shekara-shekara.)

An kafa shirin wannan matsayin “Parental Glory” a watan Mayu 2008, kuma daga ofishin shugaban kasar ne. Kasar Rasha tana ba da wannan lambar yabo ne ga iyayen da suka yi renon akalla yara bakwai kuma sun kula da lafiyar jikin iyalinsu sosai kuma illimantar da su a hanyar da ya kamata, kuma sun suturtar da su, da kuma mai da hankali ga jiye-jiye da dabi’unsu. Duk iyalin da aka ba su wannan lambar yabo, sun zama abin koyi.

Shugaban Rasha ya ba Valeriy Novik, uba mai ’ya’ya takwas lambar yabo na matsayin da ake ce da shi “Parental Glory.”

David A. Semonian, wani wakilin Shaidun Jehobah a hedkwatansu ya ce: “Wannan yabon sakamakon nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suke yi kyauta ne ya taimake iyaye da kuma ‘ya’yansu su zama mutane masu hankali ba a kasar Rasha kadai ba amma a duk duniya. Muna fatan cewa za a yi la’akari akan wannan takardar yabo da Shugaban Rasha ya bayar a lokacin da Babban Kotun Rasha za ta sake duba shawarar da ta yanke na sa wa aikin Shaidun Jehobah a Rasha takunkumi a ranar 17 ga Yuli 2017.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000