Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA YUNI, 2015
RASHA

Ana Sa Rai Za A Saurari Hukunci Mai Muhimmanci a Birnin Taganrog Ba da Dadewa Ba

Ana Sa Rai Za A Saurari Hukunci Mai Muhimmanci a Birnin Taganrog Ba da Dadewa Ba

An yi watanni biyar ke nan tun da aka sake soma yi wa wasu Shaidun Jehobah 16 shari’a a birnin Taganrog a Rasha, a watan Fabrairu na 2015. Ana yi musu barazanar ci musu tara da kuma kai su kurkuku domin sun yi hidimar ibada.

Da farko an soma shari’ar a 13 ga Mayu, 2013, bayan aka tuhume su da laifin yin ayyuka da suke nuna tsattsauran ra’ayi. Kotun ta ci wa Shaidun Jehobah guda bakwai tara kuma ta hukunta guda hudu da dauri a kurkuku na tsawon lokaci, amma alkalin ya dakatar da hukuncin. A ranar 12 ga Disamba, 2014, kotun daukaka kara ta ba da doka a sāke soma shari’ar bisa ga rokon wanda ya shigar da karar. Shaidun Jehobah suna sa rai za su ji hukuncin da kotun za ta yanke a karshen watan Yuni.