Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah suna raira waka a taronsu na Kirista a Rostov-on-Don, a kasar Rasha

22 GA SATUMBA, 2016
RASHA

SASHE NA 1

Abin da Masana Suka Fada: Kasar Rasha Tana Amfani da Dokar Yaki da Tsattsauran Ra’ayi Wajen Hukunta Shaidun Jehobah da Wayo

Abin da Masana Suka Fada: Kasar Rasha Tana Amfani da Dokar Yaki da Tsattsauran Ra’ayi Wajen Hukunta Shaidun Jehobah da Wayo

Wannan shi ne Sashe na 1 a cikin jerin ganawa mai sassa uku, wanda aka yi da shahararrun masana a kan harkokin addini da siyasa da zamantakewa da kuma masana tsarin kasar Rasha na dā da na yanzu.

ST. PETERSBURG, a Rasha​—⁠Mai Shigar da Kara a Madadin Gwamnatin Rasha yana kokarin hada Shaidun Jehobah a cikin jerin mutane masu “tsattsauran ra’ayi.” Idan kotu ta amince da bukatar Mai Shigar da Karar, za a kwace rijistar Shaidun Jehobah a kasar kuma za a hana su gudanar da ayyukan ibada a kasar Rasha baki daya. Shaidun Jehobah sun daukaka kara kuma ana sa rai kotun za ta saurare karar a ranar 23 ga Satumba, 2016.

Rasha tana tuhumar Shaidun Jehobah bisa ga dokar kasarta a kan yaki da tsattsauran ra’ayi, amma masana sun ce wannan dokar tana “cike da kurakurai,” tana “nuna wariya” kuma “ba bisa ka’ida take ba.”

Dr. Derek H. Davis

Wani tsohon darekta na J.M. Dawson Institute of Church-State Studies a Jami’ar Baylor mai suna Dr. Derek H. Davis, ya ce: “Irin tsattsauran ra’ayin da ya kamata a yaka shi ne wanda zai iya sa rayukan mutane a cikin hadari.” Ya dada da cewa: “Idan mutum yana yakar ra’ayin da ba zai jefa rayukan mutane a cikin hadari ba, shi mai tsattsauran ra’ayi ne.”

Dr. Mark Juergensmeyer

Wani darekta mai suna Dr. Mark Juergensmeyer daga Orfalea Center for Global and International Studies a Jami’ar California, Santa Barbara, ya bayyana dalilin da ya sa hukumomi suke daukan tsattsauran matakai a kan Shaidun Jehobah duk da cewa Shaidun Jehobah masu son zaman lafiya ne. Ya ce: “Hana ‘yancin yin ibada a sunan yaki da tsattsauran ra’ayi cin mutunci ne da wayo.” Kari ga haka, wani mai suna Dr. Jim Beckford daga British Academy ya ce: “Shugabannin Cocin Orthodox na Rasha suna hada baki da gwamnatin kasar don su cim ma burinsu kuma su danne duk wani addinin da suke ganin yana samun karuwa.”

Dr. Jim Beckford

Masana sun bayyana cewa babbar matsalar ita ce, an tsara dokokin Rasha a hanyar da za su ba gwamnati damar aiwatar da su a hanyar da suka ga dama. Wata kungiya mai kāre hakkin bil-adama a birnin Moscow mai suna SOVA Center ta ce: “Kamar yadda muka saba fada, yadda aka tsara dokar yaki da tsattsauran ra’ayi da kuma irin kalmomin da aka yi amfani da su sun ba gwamnatin Rasha damar cin mutuncin kungiyoyin siyasa na adawa da kuma kungiyoyi da ra’ayinsu ya bambanta da na gwamnati.

Dr. Emily B. Baran

Wata mai suna Dr. Emily B. Baran, mataimakiyar farfesa na tarihin kasar Rasha da Gabashin Turai a Jami’ar Middle Tennessee ta ce: “Ya kamata mutanen Rasha su nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnati take tsananta wa Shaidun Jehobah.” Dalilinta shi ne, “bulalar da aka bugi uwargida da ita, da ita za a bugi amarya wata rana. Ma’ana, gwamnati za ta iya kwace ‘yancin sauran mutane kuma ta wulakanta wadanda ra’ayinsu ba ta jitu da nata ba a duk lokacin da ta ga dama.”

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, 1-718-560-5000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, 7-812-702-2691