Koma ka ga abin da ke ciki

14 GA OKTOBA, 2016
RASHA

Wata Kotu a Rasha Ta Yi Watsi da Karar da Shaidun Jehobah Suka Daukaka Domin Su Kalubalanci Gargadin da Mai Shigar da Kara a Madadin Rasha Ya Aika Musu

Wata Kotu a Rasha Ta Yi Watsi da Karar da Shaidun Jehobah Suka Daukaka Domin Su Kalubalanci Gargadin da Mai Shigar da Kara a Madadin Rasha Ya Aika Musu

A ranar 12 ga Oktoba, 2016, Kotun Gunduma na Tverskoy a birnin Moscow ta yi watsi da karar da Shaidun Jehobah suka daukaka domin ana neman a rufe ofishinsu da ke kusa da birnin St. Petersburg. Mai shigar da Kara a Madadin Gwamnatin Rasha ya rubuta wasikar gargadi ne zuwa ga ofishin Shaidun Jehobah a ranar 2 ga Maris, 2016, kuma a cikin wasikar ya ce ko da yake ba ofishin ne da kansa ya aikata “ayyukan tsattsauran ra’ayi” ba, mambobinta da suke wasu yankunan kasar sun yi hakan. Saboda haka, ana neman a rufe ofishin Shaidun Jehobah na kasar da yake ofishin ne yake ja-gorar ayyukan Shaidun Jehobah a kasar Rasha. Wadannan “ayyukan tsattsauran ra’ayi” da ake tuhumar Shaidun Jehobah da yi kulle-kulle ne da hukumomin yankunan suka yi kuma sun kawo shaidar karya a kai. A lokacin da ake sauraron karar, alkalin ya ki barin Shaidun Jehobah su ba da shaida ko kuma su nuna bidiyon da ke dauke da yadda hukumomin yankuna da dama suka kulla wa Shaidun Jehobah makirci ta wajen saka musu haramtattun littattafai a cikin majami’unsu.

Shaidun Jehobah za su daukaka kara zuwa Moscow City Court. Idan wannan kotun ta kama Shaidun Jehobah da laifi, Mai shigar da Kara wa gwamnatin kasar zai aikata abin da yake barazanar yi kuma hakan zai iya hana Shaidun Jehobah a kasar Rasha gudanar da addininsu. Sakamakon wannan hukuncin da kuma sababbin shaidar da hukumomi suka kulla, zai yiwu Mai shigar da Karar ya dauki matakan rufe ofishin Shaidun Jehobah na kasar Rasha.