Koma ka ga abin da ke ciki

9 GA FABRAIRU, 2018
TAIWAN

Girgizar Kasa ta Auku a Taiwan

Girgizar Kasa ta Auku a Taiwan

A daren ranar Talata, 6 ga Fabrairu, girgizar kasa ta auku a kusa da gabashin tekun Taiwan. An ruwaito cewa akalla mutane 6 ne suka mutu, kuma fiye da 250 sun jikata. Kari ga haka, ba a ga mutane 76 ba.

Babu wani mai shela da ya mutu ko ya ji rauni sanadiyyar wannan girgizar kasa. Amma, girgizar ta bata ofishin da ake fassara yaren Amis (yaren wasu ʼyan kasar Taiwan) da kuma wata Majami’ar Mulki da ke birnin Hualien inda girgizar kasar ta fi yin barna. Kari ga haka, girgizar kasar ta bata wurin da wasu mafassaran ke zama kuma hakan ya sa aka kaurar da su daga wurin. Nan da nan, ’yan’uwa suka shirya wurin da wadanda bala’in ya shafa za su zauna. Ban da haka, ofishinmu da ke Taiwan na kokarin yi wa ’yan’uwan tanadin bukatunsu.

Muna addu’a ’yan’uwanmu da wannan bala’i ya shafa su sami kwanciyar hankali a wannan mawuyacin lokaci, kuma muna addu’a cewa wadanda ke kula da su za su “zama kamar mafaka daga iska.”—Ishaya 32:2.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Taiwan: Chen Yongdian, +886-3-477-7999