11 GA AGUSTA, 2017
TAIWAN
An yi Nasarar Soma Wani Tsarin Hidimar Farin Hula a Taiwan
A shekara ta 2000, kasar Taiwan ta fito da wani fannin hidimar farin hula da zai sa mutane su yi wa kasar su hidima ba tare da sun saba wa addininsu ba. A wannan sabon tsarin da aka fitar, wadanda lamirinsu ba ya yarda su yi aikin soja ba za su iya yin aiki a asibiti da wuraren da ake jinyar tsoffofi da dai sauransu. Wannan sabon tsarin yana da kyau sosai domin ya amfani mutanen Taiwan da kuma wadanda ba sa saka hannu a yaki.
Wannan bidiyon ya bayyana yadda aka fitar da wani sabon fannin hidimar farin hula a Taiwan. Bidiyon ya amsa wasu tambayoyin da mutane suka yi game da wannan hidimar da kuma abin da mutanen da ra’ayin ya shafe su suka fada game da hidimar. Wani darekta na National Conscription Agency mai suna Kou-Enn Lin ya ce: “Ina fatan wasu kasashe za su koyi darasi daga abin da muka yi wa kasarmu.”