Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa—Bidiyoyi

Ka koyi yadda za ka yi karatu da kuma koyarwa a gaban jama’a.

DARASI NA 1

Gabatarwa Mai Dadi

Ta yaya za ka ja hankalin masu sauraronka ga abin da kake so ka koya musu?

STUDY 2

Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa

Me za ka yi don ka kwantar da hankalin masu sauraronka ya yayin da kake musu magana?

DARASI NA 3

Ka Yi Amfani da Tambayoyi

Ta yaya za ka yi amfani da tambayoyi don ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci wani batu, don ka sa su saurare ka, ko kuma don ka nanata muhimman darussa?

DARASI NA  4

Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace

Ta yaya za ka taimaka wa masu sauraronka su amfana daga ayoyin Littafi Mai Tsarkin da ka karanta?

DARASI NA  5

Ka Yi Karatu Sumul

Mene ne zai taimaka maka ka karanta abin da ke shafin da babban murya?

DARASI NA 6

Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta

Mene ne za ka yi sa’ad da kake karanta wani nassi? Me kuma za ka iya yi don ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci dalilin da ya sa ka karanta nassin?

DARASI NA 16

Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa

Wadanne abubuwa uku ne muke bukatar mu yi don abin da muka fada ya karfafa mutane kuma ya sa su kasance da bege?

DARASI NA 17

Ka Yi Bayani Dalla-Dalla

Idan kana so masu sauraronka su fahimci abin da kake cewa, wadanne abubuwa ne za ka guje wa?

DARASI NA 18

Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin

Ta yaya za ka sa masu sauraronka tunani a kan batun da kake gaya musu kuma su koyi darussa masu muhimmanci?

DARASI NA 19

Maganarka ta Ratsa Zuciya

Ta yaya za ka taimaka wa masu sauraronka su yi abubuwa masu muhimmanci?

DARASI NA 20

Kammalawa Mai Dadi

Me ya kamata ka cim ma sa’ad da kake kammala jawabi ko wa’azi?

Mai Yiwuwa Za Ka Kuma So

LITTATTAFAI DA ƘASIDU

Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa

An shirya wannan littafin don ya taimaka muku ku kyautata yadda kuke karatu da magana da kuma koyarwa.