6-12 ga Yuni
ZABURA 34-37
Waƙa ta 95 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Nagarta”: (minti 10)
Za 37:1, 2—Ka mai da hankali ga bautarka ga Jehobah, ba ga nasarar da miyagu suke yi ba (w03 12/1 21-22 sakin layi na 3-6)
Za 37:3-6—Ka dogara ga Jehobah, ka yi nagarta kuma ka sami albarka (w03 12/1 22-24 sakin layi na 7-15)
Za 37:7-11—Ka yi haƙuri, ka jira har sai Jehobah ya cire miyagu (w03 12/1 25 sakin layi na 16-20)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Za 34:18—Ta yaya Jehobah yake ɗaukan “masu-karyayyar zuciya” da waɗanda suka fid da zuciya? (w11 6/1 19)
Za 34:20—Ta yaya annabcin nan ya cika a kan Yesu? (w13 12/15 21 sakin layi na 19)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Za 35:19–36:12
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon gabatarwar mujallu, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka ƙarfafa masu shela su rubuta tasu gabatarwa.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 93
“Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa”: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki? da ke jw.org, sa’ad da kake tattauna kan maganar nan “Yadda Za Mu Cim ma Hakan.” (Ka shiga sashen LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA ƘASIDU. Sai ka nemo ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Za ka ga bidiyon a ƙarƙashin darasin nan “Albishirin da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Ainihi Daga Allah Ne?”)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 17 sakin layi na 1-13
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 61 da Addu’a