RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
MUHIMMANCINSA:
Da yake mutane sukan iya ga hotuna da kuma ji maganar da ake yi a bidiyo, hakan zai iya ratsa zukatansu. Bidiyoyi sukan ja hankalin mutane kuma su sa kada su manta da abin da suka kalla. Jehobah ya kafa mana misali mai kyau wajen yin amfani da abubuwan da ake gani sa’ad da yake koyarwa.—A. M. 10:9-16; R. Yoh 1:1.
Za a iya yin amfani da bidiyoyin nan Allah Yana da Suna Ne? da Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki? da kuma Ta Yaya Za Mu San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne? sa’ad da ake tattauna darasi na 2 da 3 na ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Ƙari ga haka, za a iya ƙarfafa mutane su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro ta yin amfani da bidiyoyin nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? da Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? da kuma Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? Ban da haka ma, za mu iya yin amfani da wasu bidiyoyinmu da suke da tsawo sa’ad da muke nazari da ɗalibanmu.—km 5/13 3.
YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:
-
Ka sauko da bidiyoyin da kake so ka nuna wa maigidan tun da wuri
-
Ka shirya tambaya ɗaya ko biyu da za a sami amsarta a bidiyon
-
Ku kalli bidiyon tare
-
Ku tattauna darussan da ke ciki
KU BI SHAWARAR NAN:
-
Ka juye bayan ɗaya cikin warƙoƙinmu kuma ka je wurin da aka ce ka yi scan don ku kalli bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?
-
Ka nuna bidiyon nan Ta Yaya Za Mu San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne? kuma ka ba da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! sai ka nuna wa mutumin darasi na 3