Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 21-27

Ayuba Ya Ki Tunanin Banza

Ayuba Ya Ki Tunanin Banza

Shaiɗan yana amfani da ƙarya don ya sa bayin Jehobah a yau sanyin gwiwa. Ka duba bambancin da ke tsakanin ƙaryar da Shaiɗan ya yi da kuma yadda Jehobah yake ji kamar yadda littafin Ayuba ya nuna. Ka ambata wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka nuna maka cewa Jehobah yana kula da kai.

ƘARYAR DA SHAIƊAN YA YI

YADDA JEHOBAH YAKE JI

Allah yana murna domin bayinsa ba za su iya yin abin da zai gamshe shi ba. Babu halitta da zai iya faranta masa rai (Ayu 4:18; 25:5)

Jehobah yana daraja ƙoƙarin da muke yi (Ayu 36:5)

Mutane ba su da daraja a gaban Allah (Ayu 22:2)

Jehobah yana farin ciki don amincinmu kuma yana mana albarka (Ayu 33:26; 36:11)

Babu ruwan Allah ko kana da aminci ko a’a (Ayu 22:3)

Jehobah yana kula da masu adalci (Ayu 36:7)