Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 33-37

Abokan Kirki Suna Ba da Shawara Mai Kyau

Abokan Kirki Suna Ba da Shawara Mai Kyau

Sa’ad da Elihu ya saka baki a maganar, shawarar da ya ba Ayuba da kuma yadda ya bi da shi ya yi dabam da na Eliphaz da Bildad da kuma Zophar. Ya nuna cewa shi abokin kirki ne da kuma mashawarcin da za a iya yin koyi da shi.

HALAYEN MASHAWARCI MAI KYAU

ELIHU YA KAFA MISALI MAI KYAU

32:4-7, 11, 12; 33:1

 

  • HAƘURI

  • MAI DA HANKALI

  • LADABI

 
  • Elihu ya jira waɗanda suka girme shi su gama magana kafin ya soma tasa

  • Yadda ya saurara sosai ya ba shi zarafin fahimtar batun da kyau kafin ya ba da shawara

  • Ya ambaci sunan Ayuba kuma ya yi masa magana kamar aboki

 

33:6, 7, 32

 

  • SAUƘIN KAI

  • FARA’A

  • TAUSAYI

 
  • Elihu yana da sauƙin kai da kuma kirki, kuma ya yarda cewa shi ajizi ne

  • Ya tausaya wa Ayuba don wahalar da yake sha

 

33:24, 25; 35:2, 5

 

  • LA’AKARI

  • KIRKI

  • TSORON ALLAH

 
  • Elihu ya nuna wa Ayuba cewa ra’ayinsa bai dace ba kuma ya yi hakan da sassauci

  • Elihu ya taimaka wa Ayuba ya ga cewa ba adalcinsa ba ne ya fi muhimmanci

  • Shawara mai kyau da Elihu ya ba Ayuba ta taimaka masa ya karɓi shawarwarin da Jehobah ya ba shi da hannu bibbiyu