Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

Rarraba Takardun Gayyata na Taron Yanki

Rarraba Takardun Gayyata na Taron Yanki

A kowace shekara, muna ɗokin moran abubuwan da aka shirya mana a taron yanki. Amma ya kamata mu gayyato mutane da yawa zuwa wannan taron domin su ga alherin Jehobah. (Za 34:8) Kowane rukunin dattawa zai tsai da shawara a kan yadda zai fi dacewa a yi amfani da takardun.

ABUBUWAN DA ZA A YI LA’AKARI DA SU

  • Yaushe za mu halarci taron?

  • Yaushe ne za a soma rarraba takardun a yankinmu?

  • A waɗanne ranaku ne za a fita rarraba takardun?

  • Mene ne nake so in cim ma a wannan kamfen ɗin?

  • Su waye ne nake so in gayyato zuwa taron?

ME ZA KA CE?

Bayan ka gai da masu gida, za ka iya ce:

“Muna rarraba wannan takardar a duk faɗin duniya don mu gayyaci mutane zuwa wani taro na musamman. An rubuta kwanan wata da lokaci da kuma wurin da za a yi wannan taron a cikin takardar. Za mu so ka halarci taron.”

TA YAYA ZA KA KOMA ZIYARA?

Ko da yake maƙasudinmu shi ne mu gayyaci mutane da yawa zuwa wannan taron yankin, amma ya kamata mu koma ziyara wurin waɗanda suka saurari saƙonmu sosai.

Za ka iya ba da mujallu tare da takardun gayyatar a ƙarshen mako.