Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 22-24

Kana da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?

Kana da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?

Jehobah ya kwatanta mutane da ɓaure

24:5

  • Yahudawa masu aminci da suke zaman bauta a Babila suna kama da ɓaure mai kyau

24:8

  • Sarki Zedekiya da kuma wasu da suka yi abubuwa marasa kyau suna kama da ɓaure marar kyau

Ta yaya zan kasance da “zuciya wadda za ta san” Jehobah?

24:7

  • Idan muna nazarin Kalmar Allah da kuma bin umurninsa, Jehobah zai ba mu “zuciya wadda za ta san” shi

  • Wajibi ne mu riƙa bincika zuciyarmu kuma mu daina duk wani halin da zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah

Ka yi la’akari da wannan: Shin ina da “zuciya wadda za ta san” Jehobah? Ta yaya zan kasance da irin wannan zuciyar?