Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabce Su da Kyau

Ku Marabce Su da Kyau

Su wane ne za mu marabtar da kyau? Duka sababbin mutanen da suka zo taronmu da kuma waɗanda suka daɗe ba su halarci taro ba. (Ro 15:7; Ibr 13:2) Ko ‘yan’uwanmu da suka zo daga wata ƙasa ko kuma waɗanda suka yi shekaru da yawa ba su zo taro ba. Idan kai ne a irin wannan yanayin, yaya za ka ji in aka marabce ka da kyau? Za ka yi farin ciki sosai ko ba haka ba? (Mt 7:12) Don haka, zai yi kyau ka gaisa da mutane a Majami’ar Mulki kafin a soma taro da kuma bayan an gama taro. Hakan yana ƙara sa mu jin daɗin taro sosai kuma yana ɗaukaka Jehobah. (Mt 5:16) Wataƙila ba zai yiwu mu gaisa da kowa ba. Amma mutane za su yi farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu gaishe su. *

Ba sai a taron Tunawa da Mutuwar Yesu ne kawai za mu marabci mutane da kyau ba. Amma muna bukatar yin hakan a kowane lokaci. Idan sababbi suka ga yadda muke ƙaunar juna, hakan zai motsa su su ɗaukaka Jehobah kuma su soma bauta masa.Yoh 13:35.

^ sakin layi na 3 Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun hana mu gaisawa da waɗanda aka yi musu yankan zumunci da suka halarci taro.1Ko 5:11; 2Yo 10.