LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Afrilu 2018
Yadda Za Mu Yi Wa’azi
Tattaunawa da yawa game da Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za mu yi farin ciki a rayuwa.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Bambanci da Kuma Alakar da Ke Tsakanin Idin Ketarewa da Jibin Maraice
Ko da yake Idin Ketarewa ba ya wakiltar Jibin Maraice na Ubangiji, amma akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya daga Idin Ketarewan.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Je ku Taimaki Mutane Su Zama Mabiyan Yesu—Me Ya Sa, A Ina, Ta Yaya?
Neman almajirai yana nufin koyar da mutane su riƙa bin dukan abin da Yesu ya umurce mu. Umurnin da aka ba mu na yin wa’azi ga mutane ya kunshi koyar da mutane su bi koyarwar Yesu kuma su bi misalinsa.
RAYUWAR KIRISTA
Wa’azi da Koyarwa Suna da Muhimmanci Wajen Mai da Mutane Almajiran Yesu
Yesu ya umurci mabiyansa su je su nemi almajirai. Me hakan ya kunsa? Ta yaya za mu taimaka wa mutane su zama abokan Jehobah?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“An Gafarta Maka Zunubanka”
Mene ne muka koya daga mu’ujizar da Yesu ya yi a littafin Markus 2:5-12? Ta yaya wannan labarin zai taimaka mana mu jimre sa’ad da muke rashin lafiya?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Warkarwa a Ranar Assabaci
Me ya sa abin da malaman addinin Yahudawa suka yi ya sa Yesu bakin ciki? Wadanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu sani ko muna da tausayi kamar Yesu?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Yesu Yana da Ikon Tayar da Kaunatattunmu da Suka Mutu
Idan muna tunani a kan labaran Littafi Mai Tsarki game da wadanda aka ta da su daga mutuwa, hakan zai sa mu kara gaskata da alkawarin tashin matattu.
RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Amfani da Littattafai da Bidiyoyinmu na Wa’azi da Kyau
Idan muna son mu koyar da mutane, ya kamata mu san yadda za mu yi amfani da littattafai da bidiyoyinmu na wa’azi da kyau. Wane littafi ne ya fi muhimmanci a cikin littattafan da muke amfani da su a wa’azi? Ta yaya za mu kyautata yadda muke amfani da littattafai da bidiyoyin da muke wa’azi da su?