23-29 ga Afrilu
MARKUS 3-4
Waƙa ta 77 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Warkarwa a Ranar Assabaci”: (minti 10)
Mk 3:1, 2—Malaman addinin Yahudawa suna neman su kama Yesu da laifi (jy 78 sakin layi na 1-2)
Mk 3:3, 4—Yesu ya san cewa suna ɗaukan dokokin Assabacin fiye da kima (jy 78 sakin layi na 3)
Mk 3:5—Yesu ya yi “baƙin ciki domin taurin zuciyarsu” (nwtsty na nazari)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mk 3:29—Me ake nufi da saɓa wa ruhu mai tsarki, kuma mene ne sakamakon yin hakan? (nwtsty na nazari)
Mk 4:26-29—Wane darasi ne muka koya daga kwatancin da Yesu ya yi game da mashuki da ya yi barci? (w14 12/15 12-13 sakin layi na 6-8)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mk 3:1-19a
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi, sai ka ba maigidan littafin da za ku riƙa nazari da shi.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 36 sakin layi na 21-22—Ka nuna yadda za a iya ratsa zuciyar ɗalibin.
RAYUWAR KIRISTA
“Wanda Yake da Kunnuwa na Ji, Shi Ji”: (minti 15) Ka bayyana abin da Markus 4:9 take nufi (nwtsty na nazari). Ka saka bidiyon nan Za Ka Zama Mai Hikima Idan Kana Karɓan Shawara. Sai ku tattauna abin da ke shafi na 46-47 na littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 6 sakin layi na 16-23
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 123 da Addu’a