30 ga Afrilu–6 ga Mayu
MARKUS 5-6
Waƙa ta 151 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yesu Yana da Ikon Tayar da Ƙaunatattunmu da Suka Mutu”: (minti 10)
Mk 5:38—Muna baƙin ciki sosai idan wani da muke ƙaunar sa ya rasu
Mk 5:39-41—Yesu yana da ikon tayar da waɗanda suka mutu (nwtsty na nazarin Mk 5:39)
Mk 5:42—Tashin matattu a nan gaba zai sa mutane “mamaki” sosai (jy 118 sakin layi na 6)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mk 5:19, 20—Me ya sa umurnin Yesu a wannan lokacin ya yi dabam da na sauran? (nwtsty na nazarin Mk 5:19)
Mk 6:11—Mene ne furucin nan “ku karkaɗe kura da ke ƙarƙashin sawayenku” yake nufi? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mk 6:1-13
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka fara bin bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Ka nuna wa maigidan dandalin jw.org.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ka yi tambaya don ziyara ta gaba.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 36 sakin layi na 23-24—Ka nuna yadda za a iya ratsa zuciyar ɗalibin.
RAYUWAR KIRISTA
“Ku Yi Amfani da Littattafai da Bidiyoyinmu na Wa’azi da Kyau”: (minti 5) Tattaunawa.
Ƙungiyar Jehobah Tana Ƙarfafa Mu: (minti 10) Tattaunawa. Ka nuna bidiyon. Bayan haka, ka yi waɗannan tambayoyin: Waɗanne matsaloli ne ɗan’uwa da ’yar’uwa Peras suka fuskata? Mene ne ya taimaka musu su jimre? Me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin ƙoƙari a ibadarmu sa’ad da muke fuskantar matsaloli?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 7 sakin layi na 1-9 da akwatin da ke shafi na 76 da kuma 78
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 72 da Addu’a