1-7 ga Afrilu
1 KORINTIYAWA 7-9
Waƙa ta 136 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Albarkar Kasancewa Marasa Aure”: (minti 10)
1Ko 7:32—Kiristoci marasa aure za su iya ƙara himma a bautarsu ga Jehobah domin ba su da ɗawainiya kamar ma’aurata (w11 1/15 17-18 sakin layi na 3)
1Ko 7:33, 34—Kiristoci ma’aurata suna damuwa “da abubuwan duniya” (w08 7/15 27 sakin layi na 1)
1Ko 7:37, 38—Kirista da bai yi aure ba don yana son ya ƙara ƙwazo a bautarsa ga Jehobah zai yi hakan fiye da wanda ya yi aure (w96 11/1 5 sakin layi na 14)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
1Ko 7:11—Wane yanayi ne zai iya sa Kiristoci ma’aurata su rabu? (lv rataye da ke shafi na 220 sakin layi na 2 zuwa shafi na 221)
1Ko 7:36—Me ya sa ya kamata Kirista ya wuce lokacin da sha’awar jima’i take da ƙarfi sosai kafin ya yi aure? (mwbr19.04-HA an ɗauko daga w00 7/15 31 sakin layi na 2)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) 1Ko 8:1-13 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace, kuma ku tattauna darasi na 4 na ƙasidar nan Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa.
Jawabi: (minti 5 ko ƙasa da hakan) w12 11/15 20—Jigo: Waɗanda Suka Zaɓi Su Kasance Marasa Aure Sun Samu Baiwa Na Yin Hakan Ta Hanyar Mu’ujiza Ne? (th darasi na 12)
RAYUWAR KIRISTA
Ka Ji Daɗin Bauta wa Jehobah Ko da Ba Ka Yi Aure Ba: (minti 15) Ku kalli bidiyon. Sa’an nan ka yi waɗannan tambayoyin: Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci marasa aure suke fuskanta? (1Ko 7:39) Ta yaya ’yar Yefta ta kafa mana misali mai kyau? Ta yaya Jehobah yake albarkar waɗanda suke bauta masa da dukan zuciyarsu? (Za 84:11) Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su iya taimaka wa ’yan’uwa marasa aure? Mene ne Kiristoci marasa aure za su iya yi don su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 5 sakin layi na 18-22 da Taƙaitawar da ke shafi na 60-61 da kuma Ƙarin Bayani na 16
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 42 da Addu’a