Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 1 KORINTIYAWA 7-9

Albarkar Kasancewa Marasa Aure

Albarkar Kasancewa Marasa Aure

7:32, 35, 38

Tun da daɗewa, Kiristoci da yawa sun gano cewa kasancewa marar aure yana kawo albarka sosai. Yana ba su damar ƙara ƙwazo a hidimarsu da yin tarayya da mutane dabam-dabam da kuma sa su kusaci Jehobah sosai.

Wasu ’yan’uwa suna wa’azi a Ostareliya, 1937; wata ’yar’uwa da ta sauke karatu a makarantar Gilead ta isa wurin da za ta yi hidima a Meziko, 1947

Wani ɗan’uwa yana wa’azi a Barazil; wasu ’yan’uwa a Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki a ƙasar Malawi

DON BIMBINI: Idan ba ka da aure, me za ka yi don ka ji daɗin bauta wa Allah?

Mene ne ’yan’uwa a ikilisiya za su yi don su ƙarfafa da kuma taimaka wa waɗanda ba su yi aure ba?