RAYUWAR KIRISTA
Ku Nemi Ilimi Daga Wurin Jehobah
MUHIMMANCINSA: Jehobah, Malami Mafi Girma yana so mu sami ilimin da ya fi kowane ilimi a duniya. Yana koya mana yadda za mu inganta rayuwarmu kyauta a yanzu da kuma a nan gaba! (Ish 11:6-9; 30:20, 21; R. Yar 22:17) Ta wajen wannan ilimin ne Jehobah yake koya mana yadda za mu yi wa mutane wa’azi.—2Ko 3:5.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
-
Ka kasance da sauƙin kai.—Za 25:8, 9
-
Ka yi amfani da koyarwar da Jehobah yake ba ka yanzu kamar aikin da ake ba wa ɗalibai a taron mako
-
Ka yi tunani a kan yadda za ka faɗaɗa hidimarka.—Fib 3:13
-
Ka ɗau wasu matakan da za su sa a daɗa koyar da kai.—Fib 3:8
KU KALLI BIDIYON NAN ALBARKUN DA KOYARWAR JEHOBAH KE KAWOWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Waɗanne matsaloli ne wasu ’yan’uwa suka shawo kansu kafin su halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki?
-
Waɗanne irin koyarwa ne ake samu a Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki?
-
Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya suka taimaka wa ɗaliban da suka zo hidima a yankinsu?
-
Mene ne mutum zai yi kafin ya cancanci zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? (kr 189)
-
Waɗanne koyarwa ne kuma kake so ka samu a ƙungiyar Jehobah?