8-14 ga Afrilu
1 KORINTIYAWA 10-13
Waƙa ta 30 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Jehobah Mai Aminci Ne”: (minti 10)
1Ko 10:13—Jehobah ba ya zaɓa mana irin jarabar da za ta same mu (w17.02 29-30)
1Ko 10:13—Wasu ma suna fuskantar irin jarabar da muke fuskanta
1Ko 10:13—Idan mun dogara ga Jehobah, zai taimaka mana mu jimre duk wata jarabar da ta same mu
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
1Ko 10:8—Me ya sa ayar nan ta ce Isra’ilawa 23,000 ne suka mutu a rana ɗaya saboda lalata, amma Littafin Ƙidaya 25:9 ya ce mutane 24,000 ne suka mutu? (mwbr19.04-HA an ɗauko daga w04 4/1 29)
1Ko 11:5, 6, 10—Wajibi ne ’yar’uwa ta ɗaura ɗankwali kafin ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban ɗan’uwa? (w15 2/15 30)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) 1Ko 10:1-17 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Ku kalli bidiyon kuma ku tattauna shi.
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 1)
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Mutumin ya ba da wata hujja da mutane a yankinku suka saba bayarwa. (th darasi na 3)
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari. (th darasi na 6)
RAYUWAR KIRISTA
‘Gaɓoɓin . . . Suna da Muhimmanci’ (1Ko 12:22): (minti 10) Ku kalli bidiyon.
“Yaya Za Ka Yi Shiri don Tunawa da Mutuwar Yesu?”: (minti 5) Jawabi. Ka ƙarfafa ’yan’uwa su yi amfani da lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu don su yi tunani a kan manufar taron kuma su ƙara nuna godiya don ƙaunar da Jehobah da Ɗansa suka nuna mana.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 6 sakin layi na 1-8 da Ƙarin Bayani na 17 da 18
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 31 da Addu’a