Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Yaya Za Ka Yi Shiri Don Tunawa da Mutuwar Yesu?

Yaya Za Ka Yi Shiri Don Tunawa da Mutuwar Yesu?

Daga wannan shekarar, za mu riƙa samun ƙarin lokaci da za mu yi shiri don taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Idan taron ya faɗi a ranar Litinin zuwa Jumma’a, ba za a yi taron Tsakiyar mako ba. Idan kuma ya faɗi a ranar Asabar ko Lahadi, ba za a yi Jawabi ga Jama’a ko nazarin Hasumiyar Tsaro ba. Ta yaya za ka yi amfani da ƙarin lokacin da kake da shi da kyau? Kamar yadda Kiristocin ƙarni na farko suka saba yi, dole ne mu yi wasu shirye-shirye kafin wannan taron mai muhimmanci. (Lu 22:​7-13; km 3/15 1) Amma akwai wasu abubuwa kuma da za mu iya yi don mu amfana sosai daga wannan taron. Ta yaya za mu yi hakan?

  • Ka yi tunani a kan muhimmancin halartar taron.​—1Ko 11:​23-26

  • Ka yi addu’a kuma ka yi tunani a kan yadda dangantakarka da Jehobah take.​—1Ko 11:​27-29; 2Ko 13:5

  • Ka karanta kuma ka yi bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka bayyana manufar taron.​—Yoh 3:16; 15:13

Wasu ’yan’uwa sukan karanta kuma su yi bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki da ake sakawa a cikin Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana a lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu. Wasu kuma sukan karanta ayoyin da ke akwati da kuma taswirar da ke ƙasa. Har ila, wasu kuma sukan yi nazarin talifofin Hasumiyar Tsaro da suka yi bayani game da taron Tunawa da Mutuwar Yesu da kuma ƙaunar da Allah da Ɗansa suka nuna mana. Ko da wani irin littafi ko talifi ne ka zaɓa ka yi nazarinsa, fatanmu shi ne ya taimaka maka ka ƙara kusantar Jehobah da kuma Ɗansa.