Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 32-33

Ka Yi Kokawa Domin Ka Sami Albarka?

Ka Yi Kokawa Domin Ka Sami Albarka?

32:24-28

Don mu sami albarkar Jehobah, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sa bautarsa farko a rayuwarmu. (1Ko 9:​26, 27) Idan muna bauta ma Jehobah, mu sa ƙwazo sosai kamar yadda Yakub ya yi sa’ad da yake kokawa da mala’ika. Za mu nuna cewa muna son albarkar Jehobah ta wajen . . .

  • Yin shiri da kyau kafin mu halarci taro

  • Zuwa wa’azi a kai a kai

  • Yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka ma ’yan’uwa

Ko a wane yanayi kake ciki, ka riƙa roƙon Jehobah ya taimaka maka kuma ya albarkaci ƙoƙarin da kake yi don ka bauta masa.

KA TAMBAYI KANKA, ‘A wane fanni na rayuwa ne nake bukatar in ƙara ƙoƙari don Jehobah ya albarkace ni?’