Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Me Ya Fi Muhimmanci a Gare Ni?

Me Ya Fi Muhimmanci a Gare Ni?

Yakub ya yi kokawa da mala’ika domin ya sami wani abu mai muhimmanci, wato albarkar Jehobah. (Fa 32:​24-31; Ho 12:​3, 4) Mu kuma fa? Muna yin iya ƙoƙarinmu mu yi biyayya ga Jehobah domin mu sami albarkarsa? Alal misali, idan muka sami aikin da zai hana mu zuwa taro, me za mu yi? Idan muka bauta ma Jehobah da dukan ƙarfinmu da dukan lokacinmu da kuma dukiyarmu, zai zubo mana “albarku masu yawan gaske.” (Mal 3:10) Zai ja-gorance mu, ya kāre mu kuma ya biya bukatunmu.​—Mt 6:33; Ibr 13:5.

KU KALLI BIDIYON NAN KA YI ƘOƘARI KA CIM MA MAKASUDAN DA KA KAFA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya abin da ’yar’uwar take so ya zama mata jarraba?

  • Ta yaya aikinmu zai iya zama mana jarraba?

  • Me ya sa Timoti ya ci gaba da kafa makasudai ko da yake shi mai ibada ne sosai?​—1Ti 4:16

  • Wane abu ne ya fi muhimmanci a gare ka?

    Ta yaya za mu nuna “aikin da ya fi muhimmanci” a gare mu?