13-19 ga Afrilu
FARAWA 31
Waƙa ta 112 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yakub da Laban Sun Yi Alkawarin Zaman Lafiya”: (minti 10)
Fa 31:44-46—Yakub da Laban sun tara duwatsu kuma sun ci abinci a kai. Hakan na wakiltar alkawarin da suka yi (mwbr20.04-HA an ɗauko daga it-1 883 sakin layi na 1)
Fa 31:47-50—Sun saka ma wurin suna Galeyed da Mizfa (mwbr20.04-HA an ɗauko daga it-2 1172)
Fa 31:51-53—Sun yi alkawari cewa za su zauna lafiya da juna
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 31:19—Mene ne wataƙila ya sa Rahila ta sace gunkin mahaifinta? (mwbr20.04-HA an ɗauko daga it-2 1087-1088)
Fa 31:41, 42—Me labarin Yakub ya koya mana game da yadda za mu yi sha’ani da shugabanninmu na aiki “marasa tausayi”? (1Bi 2:18; w13 3/15 21 sakin layi na 8)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 31:1-18 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon, sai ka yi tambayoyin nan: Ta yaya ’yar’uwar ta bayyana nassin dalla-dalla? Me ’yar’uwar ta faɗa da zai sa ta sake dawowa?
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Mutumin ya ba da wata hujja da mutane suka saba bayarwa. (th darasi na 4)
Haɗuwa ta Fari: (minti 5 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka ba da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! kuma ku soma nazarin darasi na 5. (th darasi na 8)
RAYUWAR KIRISTA
Ku Ƙarfafa Waɗanda Suka Yi Sanyi a Ibadarsu: (minti 20 ko ƙasa da hakan) Jawabin da dattijo zai yi. Ku kalli bidiyon nan Jehobah Yana Kula da Tumakinsa. Bayan haka, sai ka tattauna bayanan da ke shafi na 14 na ƙasidar nan Ka Komo ga Jehobah a hanyar da za ta ƙarfafa ’yan’uwa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 6 sakin layi na 1-14
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 146 da Addu’a