Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku “Kawar da Gumakan Allolin” Karya

Ku “Kawar da Gumakan Allolin” Karya

Yakub ya san cewa Jehobah ne kaɗai ya kamata a bauta wa, ko da yake a lokacin Jehobah bai kafa doka game da bautar gumaka ba. (Fit 20:​3-5) Shi ya sa bayan da Jehobah ya gaya wa Yakub ya koma Betel, Yakub ya gaya ma waɗanda suke tare da shi su kawar da dukan gumaka da suke wurinsu. Yakub ya binne gumakan har da ’yan kunne da suke sakawa don samun kāriya. (Fa 35:​1-4) Babu shakka, Jehobah ya ji daɗin matakin da Yakub ya ɗauka.

A yau, ta yaya za mu bauta wa Jehobah shi kaɗai? Muna bukatar mu guje wa duk wani abin da yake da alaƙa da bautar gumaka da kuma sihiri. Hakan na nufin za mu kawar da abubuwan tsafi kuma mu riƙa zaɓan nishaɗin da za mu yi. Alal misali, ka tambayi kanka: ‘Ina jin daɗin karanta littattafai ko kuma kallon fina-finan da suke nuna maita, aljanu ko kuma dodanni? Nishaɗin da nake yi yana nuna cewa tsafi da bokanci da kuma yi wa mutane asiri ba laifi ba ne? Ya kamata mu nisanta kanmu daga duk abin da Jehobah ya tsana.​—Za 97:10.

KU KALLI BIDIYON NAN “KADA KU BA SHAIƊAN DAMA,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wace matsala ce wata ɗaliban Littafi Mai Tsarki mai suna Palesa ta soma fuskanta?

  • Me ya sa yake da kyau mu nemi taimakon dattawa idan mu ko ɗalibinmu yana da matsalar da ta shafi sihiri?

  • Kada ka ba Shaiɗan dama kuma ka yi kusa da Allah. ​—Yaƙ 4:​7, 8

    Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu kawar da su idan muna so Jehobah ya kāre mu?

  • Wane mataki mai kyau ne Palesa ta ɗauka?

  • Mene ne za ka iya yi a yankinku don ka guji abubuwan da suka shafi aljanu?