ZABURA 87-91
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Ka Kasance Cikin Mabuyan Madaukaki
“Maɓuyan” Jehobah yana kāre dangantakarmu da shi
91:1, 2, 9-14
-
Idan muna so mu kasance cikin maɓuyan Jehobah a yau, dole ne mu keɓe kanmu kuma mu yi baftisma
-
Mutanen da ba su dogara ga Allah ba ba su san wannan maɓuyan ba
-
Mutanen da ke maɓuyan Jehobah ba sa barin kome ko kuma kowa ya raunana imaninsu da kuma ƙaunarsu ga Allah
‘Mai farautanʼ yana ƙoƙarin ɗana mana tarko
91:3
-
Tsuntsaye suna da wayo da kuma wuyan kamawa
-
Masu farautar tsuntsaye suna lura da tsuntsaye sosai don su san yadda za su kama su
-
Shaiɗan, wanda shi ne “mai-farauta,” yana neman dabaru iri-iri da zai yi amfani da su wajen sa bayin Jehobah su daina bauta masa
Dabaru huɗu da Shaiɗan yake amfani da su:
-
Tsoron Mutum
-
Kayan Duniya
-
Nishaɗi Marar Kyau
-
Saɓani