RAYUWAR KIRISTA
Ku Koyar da Gaskiya
Za a soma saka wani sabon fasalin gabatarwa mai jigo “Ku Koyar da Gaskiya” a Littafin Taro don Rayuwar Kirista daga watan Satumba. Maƙasudinmu shi ne mutane su san gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da tambaya da kuma nassi.
Idan muka sami wani da ya so saƙonmu, za mu iya ba shi warƙa ko mujalla ko littafi ko kuma mu nuna masa wani bidiyo da ke dandalin jw.org/ha don hakan zai ba mu zarafin koma ziyara. Zai dace mu koma ziyara wajensa bayan ʼyan kwanaki don mu ci gaba da tattaunawar. Za a riƙa yin amfani da taƙaitawa da ke littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? wajen shirya wannan sabon gabatarwa da kuma aikin da ɗalibai suke yi a taro. Za a sami ƙarin tambayoyi da nassosi a wurin da za su taimaka mana mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai wajen koma ziyara da kuma nazari da mutane.
Hanya ɗaya ce kawai za ta bishe mu zuwa samun rai. (Mt 7:13, 14) Da yake muna yi wa mutanen addinai da al’adu dabam-dabam wa’azi, wajibi ne mu yi amfani da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da za ta ratsa zuciyarsu sosai. (1Ti 2:4) Yayin da muke koyan hanyoyi da yawa na yin wa’azi da kuma kyautata ‘fassara maganar gaskiya daidai,ʼ za mu ji daɗin yin wa’azi sosai kuma za mu yi nasara.—2Ti 2:15, Littafi Mai Tsarki.