27 ga Agusta–2 ga Satumba
LUKA 23-24
Waƙa ta 130 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Riƙa Gafarta wa Mutane”: (minti 10)
Lu 23:34—Yesu ya gafarta wa sojojin Roma da suka rataye shi a kan gungume (cl 297 sakin layi na 16)
Lu 23:43—Yesu ya gafarta ma wani ɓarawo (g 2/08 11 sakin layi na 5-6)
Lu 24:34—Yesu ya gafarta wa Bitrus (cl 297-298 sakin layi na 17-18)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Lu 23:31—Mene ne Yesu yake magana a kai a wannan ayar? (“ga ɗanyen itace, . . . in ya bushe” bayanin Lu 23:31 a nwtsty)
Lu 23:33—Mene ne ya tabbatar mana da cewa wataƙila a zamanin dā ana kafa wa mutum ƙusa sa’ad da ake rataye shi a kan gungume? (“Ƙusa a ƙashin sawun wani” duba hoton Lu 23:33 a nwtsty)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Lu 23:1-16
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka fara da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke wa’azi da su da ya dace da yanayinsa.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 4 sakin layi na 3-4
RAYUWAR KIRISTA
“Ba Don Kai Kaɗai Yesu Ya Mutu Ba”: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Ka Kyautata Halinka!
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 12 sakin layi na 1-8
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 82 da Addu’a