Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ba Don Kai Kadai Yesu Ya Mutu Ba

Ba Don Kai Kadai Yesu Ya Mutu Ba

Yesu ya mutu a madadin ’yan Adam ajizai. (Ro 5:8) Hakika, muna wa Yesu matuƙar godiya don abin da ya yi mana. Amma a wasu lokuta, muna bukatar mu riƙa tuna cewa ba don mu kaɗai ne Yesu ya mutu ba, amma har da ’yan’uwanmu. Ta yaya za mu ƙaunaci ’yan’uwanmu ajizai kamar yadda Yesu ya yi? Na farko, mu riƙa yin abokanta da mutane dabam-dabam ba kawai waɗanda ala’adarmu ɗaya ba. (Ro 15:7; 2Ko 6:​12, 13) Na biyu, mu mai da hankali sosai don kada mu yi ko faɗi abubuwan da za su ɓata ma wasu rai. (Ro 14:​13-15) Na uku shi ne, mu riƙa saurin gafarta wa ’yan’uwanmu idan suka yi mana laifi. (Lu 17:​3, 4; 23:34) Idan muna yin hakan, Jehobah zai sa mu kasance da salama da kuma haɗin kai a ikilisiya.

KU KALLI BIDIYON NAN KA KYAUTATA HALINKA!, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Yaya ’Yar’uwa Miki ta ji da farko game da ’yan’uwan da ke ikilisiyarsu?

  • Me ya sa ta canja ra’ayinta?

  • Ta yaya misalin Yesu ya taimaka wa ’Yar’uwa Miki ta canja ra’ayinta? (Mk 14:38)

  • Ta yaya Misalai 19:11 take taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwanmu?