Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

AWAKE!

Tambaya: Yawancin mutane suna so su kasance da ƙoshin lafiya. Me kake ganin za mu yi don mu rage yin rashin lafiya?

Nassi: Mis 22:3

Abin da Za Ka Ce: Wannan mujallar Awake! ta tattauna matakai masu kyau da za mu iya ɗauka don mu rage yin rashin lafiya.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Shin wane ne sanadiyyar wahalar da muke sha, Allah ne ko wani abu dabam?

Nassi: Ayu 34:10

Gaskiya: Allah ba shi ne sanadiyyar wahalar da muke sha ba. Amma wahalar da muke sha tana faruwa ne saboda Shaiɗan ko zaɓi marar kyau da muka yi ko kuma kasancewa a wani wuri a lokacin da bai dace ba. Sa’ad da muke shan wahala, Allah zai taimaka mana domin yana kula da mu sosai.

ME YA SA ZAI DACE MU YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI? (Bidiyo)

Tambaya: Shin kana ganin Allah ne yake mulkin duniya? [Ka bari ya ba da amsa.] Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa zai iya sa ka mamaki. Bidiyon da zan nuna maka ya bayyana hakan. [Ka nuna masa bidiyon.]

Abin da Za Ka Ce: Babi na 11 na littafin nan ya nuna dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala ta ci gaba da kuma yadda zai kawo ƙarshen ta. [Ka ba da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?]

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.