Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

“Ga Ni; Ka Aike Ni!”

“Ga Ni; Ka Aike Ni!”

Ya kamata mu yi koyi da halin sadaukarwar da Ishaya ya nuna. Ko da yake bai san cikakken bayani game da aikin da aka ba shi ba, ya nuna bangaskiya kuma nan da nan ya amince ya yi aikin. (Ish 6:8) Za ka iya yin wasu canje-canje a rayuwarka don ka yi hidima a inda ake bukatar masu shela sosai? (Za 110:3) Babu shakka, kana bukatar ka yi ‘lissafi’ sosai kafin ka soma wannan hidimar. (Lu 14:27, 28) Amma ka kasance a shirye ka yi sadaukarwa don yin wa’azi. (Mt 8:20; Mk 10:28-30) Kamar yadda aka nuna a bidiyon nan Ƙaura Zuwa Inda Ake da Bukata Sosai, albarkar da muke samu a hidimar Jehobah ta fi duk wata sadaukarwar da muka yi.

BAYAN KUN KALLI BIDIYON, KU AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Waɗanne sadaukarwa ne iyalin Williams suka yi don su yi hidima a Ecuador?

  • Waɗanne abubuwa ne suka yi la’akari da shi sa’ad da suke tunanin yin hidimar?

  • Waɗanne albarku ne suka samu?

  • A ina ne za ka iya samun ƙarin bayani game da yin hidima a inda ake da bukata?

KU TATTAUNA WAƊANNAN TAMBAYOYIN A IBADARKU TA IYALI:

  • A matsayinku na iyali, ta yaya za ku iya faɗaɗa hidimarku? (km 11/11 5-7)

  • Idan ba za ku iya yin hidima a inda ake da bukata ba, a waɗanne hanyoyi ne za ku iya taimaka wa ikilisiyarku? (w16.03 23-25)