RAYUWAR KIRISTA
Koyarwar Allah Tana Sa Mu Daina Nuna Wariya
Jehobah ba ya nuna bambanci. (A. M. 10:34, 35) Yana marabtar mutane daga “cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.” (R. Yoh 7:9) Saboda haka, bai kamata mu nuna wariya ko bambanci a cikin ikilisiyar Kirista ba. (Yaƙ 2:1-4) Muna amfana sosai daga koyarwar Allah domin tana sa mutane su canja salon rayuwarsu kuma su kasance da salama a ƙungiyar Jehobah. (Ish 11:6-9) Yayin da muke aiki tuƙuru don mu daina nuna wariya, muna nuna cewa muna yin koyi da Allah.—Afi 5:1, 2.
KA KALLI BIDIYON NAN JOHNY DA GIDEON: DĀ SU MAƘIYA NE, YANZU KUMA ‘YAN’UWA. BAYAN HAKA, KA AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Me ya sa sanin Allah ya fi ƙoƙarin da ‘yan Adam suke yi don su magance nuna bambanci da wariya?
-
Me kake sha’awa sosai game da ‘yan’uwancin da muke morewa a dukan duniya?
-
Ta yaya muke girmama Jehobah idan mun kasance da haɗin kai?