ISHAYA 1-5
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |“Ku Zo, Mu Hau Zuwa Dutsen Ubangiji”
2:2, 3
“A cikin kwanaki na ƙarshe” |
Zamanin da muke ciki yanzu |
“Dutse na gidan” Jehobah |
Bauta ta gaskiya da aka ɗaukaka sosai |
“Al’ummai duka kuma za su gangaro wurinsa” |
Waɗanda suke koyan gaskiya suna da haɗin kai |
“Mu hau zuwa dutsen Ubangiji” |
Masu bauta ta gaskiya suna kiran wasu so zo su yi bauta tare |
“Za ya koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa” |
Jehobah yana amfani da Kalmarsa wajen koyar da mu da kuma taimaka mana mu bi umurninsa |
2:4
“Ba kuwa za a ƙara koyon yaƙi nan gaba ba” |
Ishaya ya kwatanta yadda za a mayar da kayan yaƙi su zama na noma kuma hakan ya nuna cewa mutanen Jehobah za su kasance da salama. Waɗanne irin kaya ke nan? |
“Takubansu su zama garmuna” |
1 Ana amfani da garma wajen yin huɗa. Kuma ana yin wasu da ƙarafa.—1Sam 13:20 |
“Māsunsu kuma su zama lauzuna” |
2 Lauje wani irin kayan aiki ne da aka yi da ƙarfe da kuma katako. Ana amfani da shi wajen yanka amfanin gona.—Ish 18:5 |